Wakokin Hausa

Sabuwar Wakar Isah Ayagi Arewa Mu farka Audio Mp3.

Wakar Isah Ayagi Arewa Mufarka Official Music Audio.

Wakar Isah Ayagi Arewa Mu_farka Audio Mp3 ina masoyan wakokin shahararren mawakin Hausa nan Isah Ayagi tauna ya saki wata sabuwar wakarsa mai suna arewa Mu farka.

Domin nunawa gwamnati halin da yan Nigeria suke ciki na matsalar tsaro dake samun arewacin Najeriya tsawon lokaci har zuwa yanzu wanda hakan yana daya daga cikin dalilan dake kawo rashin cigaba.

Maza da mata sun fito nuna rashin jin dadi da kuma rashin nuna goyon baya akan murnar cikar Nigeria shekara 63 inda yan arewa sukace babu wannan maga domin har yau Nigeria tana cikin wani hali.

Domin kuwa ana kan fama da matsalar tsaro musamman arewacin kasar ta Nigeria dan haka suna kira zuwa gwamnatin tarayya da tayi kokarin kawo karshen wannan matsala.

Kamr yadda kowa ya sani mawakin Isah Ayagi yana daya daga cikin manyan mawakan dake mutukar taka rawar gani sosai mutuka acikin wakokinsa domin bayyanawa al,ummah wasu surruka.

Domin sanin halin da rayuwa take ciki haka babu shakka mawakin ya samu lambar yabo sosai mutuka gurin bada gudunmawa gurin fadakar da al,ummah.

 

Sabuwar Wakar Isah Ayagi Arewa Mu farka official Audio Mp3.

Manyan jarumai da kuma manyan mawaka sun bada gudunmawa sosai mutuka gurin tabbatar da zan zangar lumana domin nunawa shuwagabannin kasar Nigeria.

Rashin jin dadinsu akan abubuwan dake faruwa a arewacin kasar ta Nigeria mawaka da kuma yan Film kowa ya fito dan nuna wannan rashin jin dadi akan abun dake faruwa.

 

Arewa Muna Cikin Matsala Ta Rashin Yanci Mun Kasa Fahimtar Meyer Yanci

Fuskokin wasu ’yan Arewa da aka azabtar da su amma ba a dauki mataki ba, wasu kuma aka yi garkuwa da su amma har yanzu ba a san inda suke ba.

* Shahararren marubucin siyasa Areva Dadiata ya bace.

*Wasu dalibai sun zargi wani matashi mai suna Abubakar Sabida na Jami’ar Katsina da yin soyayya da wata yarinya mai suna Joy.

*Kwanakin baya an kashe wani mai suna Abdullah, amma gwamnati ba ta dauki mataki ba.

*An yi wa yarinya Hanifa ‘yar shekara 4 kisan gilla, amma gwamnati ba ta yi komai ba.

* ‘Yan China sun kashe Umisha suka yanke mata wuya, amma gwamnati ba ta yi komai ba.

*Daliban makarantar F.U.G Gusau an tafi dasu yanzu haka suna hannun masu garkuwa da mutane amma gwamnati bata dauki mataki ba.

*A jihar Bauchi an zargi DPO da yiwa wani matashi hari wanda har ya zuwa yau iyayen yaron suna neman hakkinsu amma babu wani mataki da aka dauka.

*A jihar Yobe wasu sojoji sun kashe fitaccen malami Sheikh Goni Aissami bayan ya fita daga kan hanya.

Babu wanda a cikin rubuce-rubucen da ba a zalunta ba tukuna, kawai abin da ‘yan Arewa ke yi shi ne gudanar da zanga-zangar ta yanar gizo kuma za su yi amfani da maudu’in #Justicefor wane!

Idan za a iya tunawa a kwanakin baya wani mawaki mai suna Mobade ya rasu a jihar Legas inda majalisar tarayya ta je ta yi kokarin kwato masa hakkinsa.

Babban burinmu yanzu shine akawo karshen matsalar tsaro domin itace matsalar dake mutukar damun arewacin Najeriya a halin yanzu muna kara addu’ar Allah Ubangiji ka kawo mana karshen wannan matsala.

Wannan shine babban fatan yan Nigeria a halin yanzu dan haka mun akara kira da sauran yan kasa kan cewa lalle mufito da gaske domin tabbatar da justice ga sauran yan uwanmu dake cikin wani hali ahalin yanzu wannan shine sakon yan arewa.

Yan uwanmu mata suna hannun yan kidnapping tsawon wani lokaci domin muna kara kira ga shugabannin dan Allah ayi kokari domin karbo su wan nan na daya daga cikin bukatar mu Allah Ubangiji yasa sakon ya isa zuwa gurin daya kamata.

Mujahid Saleh Sa’ad

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button