Labarai

kadarori 10 daya kamata sabon shugaban kasa Bola Ahmad Tinibu ya bayya nawa yan Nigeria kafin ya karbi mulki ranar 29.

Abubuwan daya kamata Ku sani a mulkin Buhari.

kadarori 10 daya kamata sabon shugaban kasa Bola Ahmad Tinibu ya bayya nawa yan Nigeria kafin ya karbi mulki babu shakka kamar yadda kundin mulkin Nigeriya ya kunsa kan cewa hakkine ga kowanne dan siyasa musamman shugaban kasa ya bayyana dukkan abun daya mallaka kafin ya shiga office.

Haka kuma kamar yadda kowanne shugaban kasa yakeyi alokacin da yazo shiga office yana bayyana dukkan kadararsa haka yan kasa suke buƙatar shima sabon shugaban kasar Baba Bola Ahmad Tinibu ya bayyana kowanne dan Nigeria yaji kuma ya sani kamar yadda kundin Tsarin Mulkin ya umarci kowanne sabon shugaban kasar yayi kafin ya karbi mulki.

Babu shakka mutane masu tarin yawan gaske halin yanzu suna yiwa baba Bola Ahmad Tinibu fatan alheri haka kuma wasu na ganin kwalliya zata biya kudin sabulu, gurin kawo abubuwa masu amfanin da zasu sanya kasar cigaba sosai domin Hausawa sunce juma,ar da zatai kyau toh tun daga Laraba ake iya ganewa.

Inda a yanzu wasu da yawan mutane suna ganin kamar tabbas daga dukkan alamu wan nan juma,ar za tayi kyau, wannan shine maganganun mafiya yawan mutane ahalin yanzu.

baba Bola Ahmad Tinibu zai karbi mulkin ranar 29 ga wan nan watan da muke ciki ahalin yanzu, Allah ka bashi ikon yin dukkan abubuwan da suka dace Ameen.

arewanahiya.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button