Hausa Music

Sabuwar Wakar Deezell Namiji ft Ice prince Hamisu Breaker.

Wakar Namiji Deezell Hamisu breaker Ice prince.

Namiji ba dan goyo bane wan nan shine farko acikin ikirarin mata wanda hakan bai kamata ba domin kuwa namiji shine wanda ya kamata kowacce ta bawa girma.

Namiji bawan Allah haka namiji gatan kowacce mace dake fadin duniya mata yana da kyau ku sani cewa namiji shine dalilin zuwanku duniya haka da tai makon namiji kika samu kulawa har kika rayu kika girma har kika zama yadda kika zama ayanzu.

Dan haka yana da kyau mata ku shiga tai tayin ku namiji shine duk wani jin dadin rayuwarku kin fito daga gidan namiji, haka kuma karshe zaki koma gidan namiji, wan nan ya zama dole babu sauyi acikin maganar tabbas wadan nan mawaka sunyi kokari kwarai da gaske domin wakar tayi mutukar dadi sosai ba kadan ba.

Download Mp3

Deezell Namiji Ft Ice prince Hamisu breaker.

Wakar na dauke da Jaruman mawaka kamar haka Deezell, Hamisu breaker,Ice prince,B.O.C da dai sauran manyan mawaka masu yawan masoya sosai.

babu shakka halin yanzu wan nan waka ta namiji itace wakar dake tashe ako,ina afadin arewa baki daya wakar namiji itace waka mafi tashe acikin wan nan shekara.

Deezell ya bayyana farin cikinsa mutuka da yadda mutane suka nuna farin cikinsu da murna akan wakar dan haka masoya dama kullum farin cikinku shine muke bukata cewar mawakin Deezell mai wakar namiji.

arewanahiya.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button