Labarai

Tabbas nayi dana sanin abun da nayi Ina neman afuwar musulmi bisa kalaman da nayi masu da suka dauki fushi dani ina mai tuba agareku. inji Kashim Shettima

Tabbas nayi dana sanin abun da nayi Ina neman afuwar musulmi bisa kalaman da nayi masu da suka dauki fushi sani ina mai tuna agareku. inji Kashim Shettima

Masha Allah mun godewa Allah  labarin da muka aika tabbas ya isa kunnuwansa

Daga Abba Sani Pantami

Mataimakin shugaban Najeriya Sanata Kashim Shetima ya ce ya nemi al’ummar musulmi da su yafewa wasu kalaman da ya yi dangane da zaben shugaban majalisar dokokin Najeriya.

A cewarsa, ba a fahimci sigar maganar ba, kuma ba shi da niyyar bata sunan addininsa.

Sanata Kassim ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da BBC cewa ya yi wadannan kalamai ne saboda muradun Najeriya, duba da cewa suna da wasu bayanan sirri, bai dace ya ce uffan ba.

Bisa la’akari da yanayin ci gaban da Nijeriya ke ciki, dole ne shugabanni su tashi tsaye wajen kula da rayuwar al’ummar kasar baki daya.

Kalaman da Shettima ya yi a makon jiya ya haifar da zazzafar muhawara musamman a shafukan sada zumunta, inda aka rika sukar mataimakin shugaban kasar.

Sai dai Kashim Shettima ya ce shi musulmin gaskiya ne domin zuriyarsu sun shafe dubban shekaru a tafarkin addinin musulunci.

Duk wanda bai gamsu da maganarsa ba to ya gafarta masa, ba shi da niyyar cutar da addini.

“Ni mutum ne ba cikakke ba, don haka ina neman gafarar al’umma da Ubangijina”.

Kashim Shettima ya tunatar da cewa shi dan malamai ne, jikan malamai, don haka ba shi da niyyar tozarta wani bangare na addinin kasar.

Tabbas sakonmu ya kai inda ya kamata, kuma mun yi addu’ar Allah ya karbi tubanka, kuma Allah ya tsayar da kai har abada.

arewanahiya.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button