Inna ilaihi wainna ilaihi raju,un jirgin ruwa yayi sanadin mutuwar Mutane 8 A Zamfara Yau.

Inna ilaihi wainna ilaihi raju,un jirgin ruwa yayi sanadin mutuwar Mutane 8 A Zamfara Yau.

Hadarin Jirgin Ruwa Ya Ci Mutane Takwasa A Zamfara A Yayin Da Suka Je Nemawa Iyayensu Ruwan Sha Saboda Matsalar Ruwa Da Ake Fama Da Shi A Yankin

A yau an samu faduwar jirgin ruwa a Gangaren Gulbi dake garin Gusau jihar Zamfara, inda aka samu asarar rayuwaka maza da mata wanda adadin su zai kai mutum takwas.

Rahotanni sun nuna cewa mamatan sun je samowa iwayen su ruwan sha ne saboda matsalar ruwan sha da ya addabi cikin garin Gusau.

Tabbas halin yanzu mutan wan nan yanki suna cikin halin tashin hankali dalilin faruwar wan nan lamari inda aka rasa rayukan mutane masu tarin yawa dalilin hadarin jirgin ruwan asafiyar yau muna kara rokon Allah Ubangiji ya bawa yan uwan wadan nan mutane hakurin rashin su.

Za,ayi jana,izarsu kamar yadda addin musulunci ya bada ikon yi Allah kaji kan dukkan Musulmin Duniya da suka rigamu gidan gaskiya marasa lafiya kuma Allah Ubangijin ka basu lafiya masu lafiya kuma muna kara rokon Ubangijin yasa mudace ameen summa ameen Allah kasa mudace rayuwar duniya kenan watarana sai labari.

Wadanda suka rasu Allah ya gafarta musu, Allah ya karbi shahadarsu.

Daga Jabir Kwaccido

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button