Labarai

Qaluinnalillahi kalli cikakken videon yadda aka kama wasu kananan yara masu garkuwa da mutane a Katsina.

Dakarun sojin Najeriya sun kashe ‘yan fashin daji a Jihar Zamfara

Dakarun sojin Najeriya da ke aiki a ƙarƙashin rundunar Operation Hadarin Daji sun kashe ‘yan fashin daji uku a wani kwanton ɓauna da suka yi musu a yankunan Anka zuwa Dan Kapani a yankin ƙaramar hukumar Anka a jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin ƙasar.

Kamfanin dillancin labaran ƙasar NAN ya ambato daraktan yaɗa labarai na hukumar tsaron Manjo Janar Musa Danmadami, na bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar.

Manjo Janar Danmadami ya ce sojojin sun kuma ƙwato makamai da suka haɗar da bindiga ɗaya ƙirar PKT, da ƙirar AK- 47 guda uku tare da alburusai masu tarin yawa, da babura uku.

Sanarwar ta ce rundunar sojin ta yaba wa dakarun tare da kira ga al’umma da su riƙa bai wa jami’an sojin bayanan sirri kan ‘yan ta’addan da inda suka ayyukansu.

Jihar Zamfara na ɗaya daga cikin jihohin Najeriya da ke fama da ayyukan ‘yan fashin daji. Rahoton BBC Hausa

“Sojoji sannunku” God bless’Operation Hadarin Daji God bless HQ Nigerian Army.

arewanahiya.com

arewanahiya

Farin cikinmu shine ganin farin ciki saman fuskarku muna alfahari duku masoya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Check Also
Close
Back to top button