Uncategorized

WANI MALAMI YAYI ALKAWARIN WAYAR DA KAN AL,UMMAH MUHIMMANCI ZABEN TINIBU.

WANI MALAMI YAYI ALKAWARIN WAYAR DA KAN AL,UMMAH MUHIMMANCI ZABEN TINIBU.

Za Mu Jagoranci Wayar Da Kan Al’ummar Nijeriya A Addinance Don Ganin Sun Zabi Tinubu A 2023, Cewar Kungiyar Limamai Magoya Bayan Tinubu

Kungiyar Limaman addinin musulunci magoya bayan dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar APC, Bola Ahmad Tinubu, wato ‘National Association Of Imams Bilhaq Bola Tinubu Campaign Organisation’ sun sha alawashin cigaba da wayar da kan al’ummar musulman Nijeriya a addinance don ganin Tinubu ya yi nasarar zama shugaban kasa a zaben 2023.

A yayin tattaunawar da shafin RARIYA ta yi da shugaban kungiyar, Malam Abubakar Abdulhadi, wanda aka fi sani da Malam Mai Imani, ya bayyana cewa sun kafa kungiyar ne domin wayar da kan al’ummar musulmai kan muhimmancin zaben Tinubu a matsayin shugaban kasa.

“Za mu dinga gudanar wa’azuzzuka a masallatai da sauran wuraren ibadu domin wayar da kan jama’a domin su zabi Tinubu duba da yadda yake da kyakkyawar manufa ga Nijeriya da al’ummarta.

Kungiyar dai tana kunshe da manyan Limamai da suka fito daga bangarorin Izalah da Darika.

arewanahiya

Farin cikinmu shine ganin farin ciki saman fuskarku muna alfahari duku masoya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button