LabaraiUncategorized

RUWAN SAMA YAYI AWAN GABA DA BABBAR HANYAR ZUWA MAHAIFAR GWAMNAN JAHAR ADAMAWA.

 

RUWAN SAMA YAYI AWAN GABA DA BABBAR HANYAR ZUWA MAHAIFAR GWAMNAN JAHAR ADAMAWA.

Daga Salisu Magaji Fandalla’fih
Hanlin yanzu Ido yayi ca Kan ganin yadda za,a dauki matakin maganin matsalar wan Nan hanyar kowanne mataki za,a dauka?

Jama’a da yawa wadanda basu san hanyar garin haihuwar Gwamnan Adamawa ciba zasu yi mamaki, wasu Kuma zasu yi tunanin ƙage ne, Wanda ko da kadan ba haka bane.

Al’ummar garin ne suka gabatar da ƙorafin su, ga Wakilin jaridar Hausa Legend, inda suke roƙon Gwamna da ya taimaka ya cece su.

Kamar yadda kuke gani, Wannan hanya itace hanyar da ta doshi ƙaramar hukumar madagali daga Michika Wanda ta ratse ta garin wuro gayandi Wanda kana tsallaka ta se madagali Wanda take garin haihuwar gwamnan jihar Adamawa me ci a yanzu, Amadu Umar Fintiri.

Kafin Fintiri anyi gwamnoni guda uku Kamar, Boni (Michika), Murtala Nyako ( Mayo-belwa) da Kuma Bindow (Mubi) Wanda kaf a cikin su Babu Wanda yayi fatali da garin haihuwar sa a cewar al’ummar yankin.

Sun bayyana cewa suna fama da matsaloli da dama sakamakon rashin hanyar ga barazanar rayukan su da hanyar ke yi.

A cewar Al’ummar yankin, a yanzu basu da wani buri illa suga Gwamna Fintiri yayi musu hanyar.

Sun bukaci Gwamnan da ya taimaki halin da al’ummar ke ciki dubada ba iya Mahaifar sa ba hanyar ta haɗa garuruwa da dama.

A ƙarshe sunyi fatan Allah ya taimaki Gwamna ya bashi ikon duban halinda suke ciki dan fitar dasu daga barazanar da hanyar ke musu.

arewanahiya.com

 

arewanahiya

Farin cikinmu shine ganin farin ciki saman fuskarku muna alfahari duku masoya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button