GWAMNATIN JAHAR KANO TA SAKA DOKAR TA BACI DAN MAGANCE WATA MATSALA.
Yanzu yanzu gwamnatin Jahar kano ta dauki matakin Hana tuka adai daita sahu Dan kawo Gyara cikin jahar ta kano.
DA DUMI-DUMI: Ganduje ya haramta tuka baburan adaidaita sahu a Jihar Kano
Gwamnatin jihar Kano ta sanar da hana zirga-zirgar babura masu kafa uku da aka fi sani da A Daidata Sahu daga karfe 10:00 na dare zuwa 6:00 na safe daga ranar Alhamis 21 ga watan Yuli, 2022.
Sanarwar da Kwamishinan Yada Labarai, Malam Muhammad Garba ya fitar ta nuna cewa an cimma matsaya kan hakan ne a karshen taron tsaro na jihar.
Ya ce matakin wani bangare ne na kokarin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi a jihar.
Kwamishinan, a cikin sanarwar, ya bukaci masu tuka baburan masu kafa uku da su bi doka su daina aiki a cikin sa’o’in da aka kayyade domin jami’an tsaro za su aiwatar da dokar ba tare da yin sulhu ba.
arewanahiya.com