Labarai

Yaushe shuwagabanni kasarmu zasu zama haka?

Tambaya yaushe shuwagabanni kasarmu zasu zama irin wadan Nan masu San rayukan talakawan kamar nasu?

Kaji kasa Mai adalan shugabanni haka ya kamata kasar Nigeria ta zama Allah ya kawo Ranar da shuwagabanni zasu dunga yin abin da talakawansu suke so.

Shugaban Ƙasar Sri Lanka Na Shirin Yin Murabus Bayan Ƴan Ƙasar Sun Yi Zanga-zangar Neman Ya Sauka Daga Mulki

Daga Aliyu Adamu Tsiga
Yan kasa sun nuna BUKATAR saukar shugaban kasar su sabida shuga kuncin rayuwar da ta Kai da rashin zuwa Yara makaranta da kuma kin yiwuwar wasu Al,amuran yau da kullum kamar yadda aka Saba.

Shugaban kasar Sri Lanka, Gotabaya Rajapaksa, zai yi murabus a ranar 13 ga Yuli, sakamakon zanga-zangar da ta ɓarke a tsibirin ranar Asabar, in ji kakakin majalisar dokokin ƙasar, Mahinda Abeywardana.

A cewar Mista Abeywardana, shugaban zai ci gaba da zama a kan karagar mulki har zuwa ranar Laraba mai zuwa domin miƙa mulki cikin lumana.

Badan komai ba sai Dan Samar da zaman lafiya acikin kasar domin gujewa asarar rayuka Dan ran Dan kasar acewar shugaban yafi zamansa akan kujerar mulki.

Don tabbatar da miƙa mulki cikin lumana, shugaban ya ce zai sauka daga mulki ranar 13 ga watan Yuli, in ji Mista Abeywardana, a wata sanarwa da aka watsa ta gidan talabijin na Al Jazeera.

A watan Yuni ne dai shugaban ya dage kan kammala sauran shekaru biyu na wa’adinsa duk da wata zanga-zangar da aka kwashe watanni ana yi na neman ya yi murabus.

Mutanen Sinhal miliyan 22 na fama da matsananciyar matsalar kuɗi tare da matsanancin ƙarancin man fetur, magunguna, abinci da sauran abubuwan da suka dace a cikin hauhawar farashin kayayyaki da kuma faɗuwar darajar kuɗin ƙasar.

Mummunan ƙarancin kuɗaɗen waje ya hana shigo da kaya daga ƙasashen waje. Ƙarancin man fetur ya gurgunta tsarin sufuri a ƙasar tare da hana yara zuwa makaranta da dai sauransu.

Wadan Nan na daya daga cikin da lilan da yasa yan ksar suke GUDANAR da zanga zangar nuna rashin amincewa da halin da suke ciki da har takai da nuna kudirin barin shugaban nasu dauka daga kujerar mulkin kasar.

Irin wannan matsalar tattalin Arziƙi da zanga-zangar ta kai ga murabus ɗin Basil Rajapaksa, ɗan uwa ga shugaban kasar Sri Lanka kuma tsohon ministan kuɗi na ƙasar daga majalisar a watan Yuni da kuma ɗan uwansu Mahinda Rajapaksa, a matsayin firaminista a watan Mayu.

Ahalin yanzu kasar na cigaba da fuskantar halin kaka Ni kayi saka makon wan nan zanga zangar Amma da yiwuwar shugaban kasar zai sauka daga kujerar mulkin Dan yiwa yan kasar abun da sukeso da kuma Zan lafiyar jama,ar kasar

arewanahiya.com

arewanahiya

Farin cikinmu shine ganin farin ciki saman fuskarku muna alfahari duku masoya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button