YANZU YANZU GWAMNATIN JAHAR ZAMFARA TA ZAR TAR DA DOKA GADUKKAN WANI DAN BINDIGA.
Yanzu Yanzu Doka zatafara aiki babu kakkautawa_ Za A Fara Rataye Yan Bindiga, ‘Yan Leken Asiri, Masu Garkuwa da Mutane Da Masu Satar Shanu again A Jihar Zamfara da kewaye.
Daga Comr Abba Sani Pantami
Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle, a ranar Talata, ya rattaba hannu kan wata sabuwar doka ta yaki da ‘yan bindiga da laifuka masu alaka a jihar domin kokari da yun kurin kawo karshen matsalar tsaron dake addabar jahar tun tsawon lokaci baya.
A kar kashin dokar, wacce ta fara aiki nan take, ta tanadi hukuncin kisa ta hanyar rataya ga duk dan bindiga da laifuka masa alaka da hakan a Zamfara hukuncin hakan ya biyo bayan kinci da cinyewar matsalar dake damun mutan jahar.
Da ya ke jawabi jim kadan bayan rattaba hannu kan dokar, Matawalle ya ce dokar na cikin matakai ne na yaki da ‘yan bindiga, masu garkuwa da satar shanu a Zamfara da akayi kokarin kawo karshen shi tun tsawon lokaci baya amma hakan taki yiywuwa.
Majalisar Dokokin Jihar ta Zamfara ta amince da kudirin dokar ne a ranar Litinin 27 ga watan Yunin 2022.haka kuma tafara aiki nan take batare da bata lokaci ba.
Matawalle yace gwamnatinsa za tayi duk mai yiwuwa a karkashin doka don kare mutanen jiharsa da kuma kokarin kara kwarin guiwa dan kawo karshen matsalar.
Haka kuma yakara da cewa Zamu cigaba da bibiyan hanyoyin samar da tsaro a Zamfara babu gudu babu jada baya a karkashin mulki na.
Lalle Ya kamata wadanda ke sukar matakan da na dauka don samar da tsaro su yi la’akari da halin da muke ciki na hare-haren yan bindiga.
Kuma Su duba mutanen da ba su jiba basu gani ba da aka kashe wa, hadi da raunatawa da garkuwa da su a kullum a sassa daban na jihar,in gwamna matawalle.
Gwamnan ya kara da yace jami’an tsaro masu kare unguwanni ba su da ban banci da dakarun JTF na Borno da Amotekun a kudu maso yamma.
Kuma Yace sabuwar dokar za ta bada daman hukunta wadan da aka samu da hannu wurin hare-haren yan bindiga da laifuka masu kama da su a karkashin doka dan hakanne kadai zai kokarin kawo karshen matsalar.
Ya kara da cewa duk wanda aka samu da laifin harin yan bindiga, garkuwa, satar shanu, kungiyar asiri ko yiwa yan bindiga leken asiri zai fuskanci hukuncin kisa,babu makawa wan nan hukuncin shine ya dace dashi.
Kotun Ta kuma bada damar yanke hukuncin daurin rai da rai, daurin shekaru 20 ko 10 ba tare da zabin biyan tara ba ga wanda aka samu yana taimakawa masu aikata laifi.
Matawalle ya yaba wa majalisar jihar don jajircewa wurin yin aikinsu na doka haka kuma zumu cigaba da saka ido dan gano wasu matsal tsalu dake datan jahar ta Zamfara.
Arewanahiya.com