Labarai

WANI MATASHI YA BAYYANA IRIN ABIN ALFAHARIN DA DR RABIU MUSA KWANKWASO YAYI MASA DAMA SAURAN YAYAN TALAKAWAN JAHAR KANO.

Cewar dalibin yace tabbas Dr Rabiu Musa KwanKwaso shugabane wanda ya can canta zama ko wanne mataki nashugabanci domin irinsa sune suka can canta zama shuwa gabannin al,ummah.

Na samu damar yin Degree na na farko ne a sakamakon wannan bawan Allah wato Engr. Rabi’u Musa kwankwaso.

Na samu sakon cewar Ana Kira ga duk wani Dan asalin jihar Kano da yake da credit 5 Kuma yaci English da Mathematics sannan ya samu 180 ko sama da haka a jamb yakai takardunsa ofishin sakataren gwamnatin jiha.

Domin adalci ba,aci Yayan masu hannu da shuni ba kamar yadda wasu shuwagaban nin sukeyi shikuma sai yace Yayan talakawa kawai ake bukata cikin wan nan al,amari.


Ba tareda nasan kowa ba ko kowa ya sanni ba akai list dani, na tafi jami’ar Igbinedion University, Okada.


Dukda ita makaranta ce ta yayan gata Kuma ta kudi, Babu ASUU bare wani Abu Wai strike, haka ya biya Mana mukai karatu mu 250 a wannan makaranta.


Bazan manta ba duk bayan wata daya zuwa biyu saiya turo wakilci daga Kano sunzo sun duba lafiyarmu da Kuma Jin kokenmu. Akwai lokacin da Muka bukaci laptops domin gudanar da karatunmu acikin salo irin na zamani, acikin watan aka bawa kowanne dalibi sabuwar laptop kirar Hp (wacce ake yayi a zamanin).


Duk semester Yana ajiye Mana Naira dubu shabiyar (15,000) domin karbar litattafan karatu ba tareda ka kashe kudinka ba.

Sannan dubu sitting( 60,000) a matsayin kudin abinci da sauran bukatunka.


Ya bamu irin kulawar da iyaye suke bawa yayansu in sun turasu karatu, daga baya ma Saida yaje da kansa donya tabbatar da ingancin abinda wakilai suke fada Masa.


Tabbas irinsa muke bukata a Nigeria, saboda ilimi shine ginshikin al’umma.
Allah ya taimaki kwankwaso da kwankwasiyya.


Idan kukaga mun dage muna son kwankwaso to so muke sauran al’umma su amfana da tsarinsa kamar yadda muka amfana domin an Mana munji dadi.
Allah yayi Mana jagora.

Tabbas babu wanda ya can canci zama Shugaban kasar Nigeria idan ba Dr Rabiu Musa KwanKwaso ba Domin shi kadaine wanda zai share hawayen yan Nigeria.

Allah yasa mu dace amee.

arewanahiya

Farin cikinmu shine ganin farin ciki saman fuskarku muna alfahari duku masoya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button