Labarai

GWAMNATIN JAHAR BAUCHI TAYI GAR GADI GA MUTAN YELWA. KAN CEWA.???

Za Mu Hukunta Masu Yin Zagon Ƙasa Ga Zaman Lafiya, Gargadin Gwamna Bala Ga Al’ummar Yelwa dan tabbatar da zaman lafiya acikin jahar ta Bauchi.

Gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Abdulƙadir Muhammad ya kirayi al’umar Yelwa dake ƙaramar hukumar Bauchi da su rungumi zaman lafiya da mutunta juna inda yace gwamnatin sa na aikin tabbatar da inganta zaman takewa da walwalar al’umar jiha domin samun tabba taccen zaman lafiya tsakanin al,Umma.

Bala Muhammad yayi wannan kira ne yayin ziyarar jaje da ya kai a yankin biyo bayan hatsaniyar da ta biyo bayan rashin fahimta tsakanin mazauna yankin da a cewar sa aikin masu zagon ƙasa ga tsaro da zaman lafiya shine ya janyo faruwar abin daya fatu.

Gwamna Bala sai yayi kira ga jami’an tsaro da su tabbatar da zaƙulo tare da tabbatar da gurfarnar da waɗanda ke da hannun cikin hatsaniyar inda yace kowane rai na da darajar da ya zama wajibi a kare shi damin wan nan shine asalin hakkin daya rata ya aeuyan mu.

Daga nan sai ya umurci hukumar agajin gaggawa ta jiha da ta ɗauki rahoton asarar da aka tafka tare da samar da tallafi inda ya ƙara da cewa haɓaka zaman lafiya nauyi ne dake rataye a wuyan kowane ɗan jiha dan zaman lafiya shine ginshikin CIGABAN duk wata al,Umma.

Daga Lawal Muazu Bauchi
Me tallafawa Gwamna Bala kan kafafen yaɗa labarai na zamani.
30 Mayu, 2022.

Idan kunne yaji to tabbas jiki ya tsira akiyaye domin azauna lafiya domin duk Wanda ya kwana lafiya tabbas shi yaso Zama lafiya yafi zama dan sarki.

arewanahiya

Farin cikinmu shine ganin farin ciki saman fuskarku muna alfahari duku masoya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button