LABARI DA DUMI DUMINSA GWAMNATIN TARAYYA TA’AYYANA DUNGA CIYAR DALIBAN MAKARANTA AKULLUM.

LABARI MAI DADI: Gwamnatin Tarayya Za Ta Kashe Naira Milyan 999 A Kullum Wajen Ciyar Da ‘Yan Makaranta Milyan Goma.
Jama,a kowa na ganin hakan ba shine abun daya kamaci yan nigeria a wan nan lokacin ba akwai abubuwa masu mutukar mahimmancin da suka fi wan nan.
Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa za ta riƙa kashe naira miliyan 999 a kullum wajen ciyar ‘yan makarantar firamare miliyan 10 a kowace rana a shirin ta na ciyar da ɗalibai, wato ‘National Home Grown School Feeding Programme’ (NHGSFP) da ta ke gudanarwa a duk faɗin ƙasar nan.
Shugabar gungun ma’aikatan da ke gudanar da shirin, Hajiya Aishatu Digil, ita ce ta bayyana haka a ranar Talata a Abuja a wajen wani taro na masu ruwa da tsaki da aka yi kan hanyoyin rarraba abincin da sake duban fasalin kuɗin da ake kashewa a shirin.

Ta ce Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ta samo amincewar a riƙa kashe N100 a kan kowane yaro a kullum a shirin.
Ta ƙara da cewa daga yanzu, za a riƙa kashe N100 a kullum wajen ciyar da kowane daga ‘yan makaranta 9,990,862 ‘yan ajin firamare ɗaya zuwa aji uku da ke cikin shirin da a kullum a tsawon kwana 20 a wata, wanda jimillar kuɗin ya kama N999,086,200 a kullum.

Ta ce, “A da kafin yanzu, mu na kashe N70 ne wajen ciyar da kowane yaro, a abinci zaman ci ɗaya. Haka mu ke yi tun daga 2016, amma yanzu shugaban ƙasa ya amince a ƙara kuɗin zuwa N100.
“Mu na da masu ruwa da tsaki irin su Shirin Abinci na Majalisar Ɗinkin Duniya (World Food Programme), da Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (National Bureau of Statistics), da Hukumar Faɗakarwa ta Ƙasa (National Orientation Agency, NOA), da Ƙungiyar Inganta Abinci ta Duniya (Global Alliance for Improved Nutrition, GAIN), da Ma’aikatar Aikin Gona da ta Ilimi, da ma wasu, da za su tattauna kan hanyoyin rarrabawar.
“Mun taru a nan ne domin mu kalli hanyar da ta fi dacewa mu yi amfani da ita wajen samun alfanun shirin bisa sabon tsarin kashe kuɗi don inganta kyawun abinci da ake ba yaran.
“Lissafin kashe N100 ɗin shi ne: N70 shi ne kuɗin dukkan kayan haɗa abincin amma ban da ƙwai, sai N14 kuɗin ƙwai da za a riƙa saye ta hanyar gwamnatocin jihohi da haɗin gwiwar Ƙungiyar Makiyaya Kaji ta Nijeriya (Poultry Association of Nigeria).
“Mu na tsara fitar da ranar da za mu kira ‘Larabar Cin Ƙwai’ (‘Egg Wednesday’), inda za a riƙa ba kowane yaro da ke cikin shirin ƙwai guda ɗaya a kowace ranar Laraba; sai N10 ta ladar masu girki, N5 da N6 na tabbatar da lafiyar abinci wanda za a riƙa ba masu girkin, da kuma naira ɗaya ta tabbatar da inganci, wadda za a ba jami’ai masu sa ido, wanda wannan zaɓi ne.”
Digil ta ce shirin zai tabbatar da an tsame muggan halayen aiwatarwa, ta ƙara da cewa ma’aikatar na so ta kawo gyare-gyare domin yin aikin cikin gaskiya ba tare da zamba cikin aminci ba.

Ta ce, “Bayan wannan taron, za mu tattaro shawarwarin masu ruwa da tsaki, sannan mu miƙa su ga minista saboda mu aiwatar da sabon tsarin kuɗin ciyarwar, wanda zai fara daga wannan watan.”
A nasa tsokacin, Dakta Umar Bindir, wato jagoran aiwatar da Shirin Inganta Rayuwa na Ƙasa (National Social Investment Programme), ya ce shirin ba haƙƙin Gwamnatin Tarayya ita kaɗai ba ne dole harda state government aciki suma sai sunsa hannu ana magana akan duka jama,ar kasane.
Bindir ya ce domin bada cikon N30 da zai zama N100 wajen ciyar da ‘yan makarantar, ya zama wajibi a tuntuɓi masu ruwa da tsakin.
Manajan shirin na NHGSFP a Jihar Sakkwato, Malam Musa Abubakar, ya ce ‘yan makaranta da iyayen su su na murna da N70 ɗin da aka riƙa kashewa wajen ciyar da kowane yaro.
Ya ce, “To amma yanzu da aka yi ƙari zuwa N100, dukkan su za su yi farin ciki domin hakan zai ƙara yawan masu shiga makaranta.”
Babban Jami’in Shirye-Shirye na hukumar NOA, Chika Ebogha, ya ce N100 da za a kashe wajen ciyar da kowane yaro ya dace ƙwarai.

Mista Ebogha ya yi kira ga Aishatu Digil da ta ƙara maida hankali ga ɓangaren aiwatarwa kamar yadda aka tsara a jihohin da su ke da matsaloli, ya ƙara da cewa a shirye NOA ta ke ta taimaka wajen sa ido da yin nazari kan shirin a dukkan faɗin ƙasar nan.
Shi kuma Mista Kingsley Anikwe daga Ma’aikatar Aikin Gona da Inganta Yankunan Karkara ta Tarayya, shawara ya bayar cewa a bada ƙwarin gwiwar yin gandun makaranta a makarantu domin su riƙa noma kayan abinci.
Ita ma Manajar Shoɗirye-Shirye ta ƙungiyar GAIN, Irowa Irabor, cewa ta yi ƙungiyar tata za ta riƙa bada ƙwaƙƙwarar shawara da horo ga masu aiwatar da shirin.
Miss Irabor ta ce ƙungiyar GAIN na da sha’awa kan tsarin ‘Larabar Cin Ƙwai’, sannan ƙungiyar za ta tallafa wajen fito da tsarin gani da ido a shirin a dukkan jihohi.

Shi kuma Onallo Akpa, wato Darakta-Janar na Ƙungiyar Makiyaya Kaji ta Nijeriya, ya yi kira da a yi kyakkyawan haɗin gwiwa da ƙungiyar wajen tabbatar da aiwatar da shirin na ‘Larabar Cin Ƙwai’.
Sai dai kuma wasu masu ruwa da tsakin sun bada shawarar cewa ya kamata gwamnatocin jihohi su jawo wasu cikin shirin, su ka ce a riƙa dafa abincin a cikin harabar makaranta sannan kuma a riƙa tantance manoman.
Shin yanzu menene ara,ayin ku kan wan nan kudiri na gwamnati.
