HAMZA ALMUSTAPHA YAYI CIKAKKEN BAYANI KAN DALILIN RASHIN TSARAN NIGERIA.
Da Gangan Aka Kirkiri Kungiyoyin Ta’addanci Irin Su Boko Haram Da Masu Garkuwa Da Mutane Don Tada Hankulan Al’umma Saboda A Sace Dukiyar Kasa, Cewar Mejo Hamza Almustapha
Daga Bappah Haruna Bajoga

Dogarin Marigayi tsohon shugaban kasa Janar Sani Abacha, wato Mejo Janar Hamza Almustapha yace, da gangan aka kirkiri kungiyoyin ‘yan ta’adda kamar Boko Haram da masu garkuwa da mutane don tada hankalin al’umma saboda sace arzikin kasa.
Hamza Almustapha yayi wannar magana, da kuma sauran wasu dumbin maganganu a kan lamuran kasar nan musamman na tsaro a sashen Hausa na BBC a cikin Shirin Gane Mini Hanya.

Ya kara cewa yankin Dajin Sambisa na jihar Borno akwai ma’adanan kasa da ake diba ake tafiya da su, kuma a yankin Zamfara ma da sauran wasu yankuna so ake a share mutanen wajen a zo a dinga dibar arzikin zinari ana tafiya da shi.
Sannan Kuma Yace akoi wasu su 6 wadanda suke kawo cikas a lamuran kasar nan, ya kwatanta su da cewa kamar Gara ce wacce ta kama Itace haka suka kama Nigeria suna gurgurawa, idan zasu huta na watanni shida talakawan Nigeria zasu samu sa’ida da hutawa. Akoi wadanda suke kawo wa kasar matsaloli daga cikin kasar, sannan akoi daga ketare a binciken da Hamza El-mustapha yace yayi.
Hakan kuma ya ce rashin tsoro, da kuma jajircewar Shugabanni ne zai kawo karshen matsalolin kasar nan, wanda El-mustapha ya nuna cewa akoi wasu kasashen da suka fada cikin cakwakiya amma samun jajircewar shugabanni tasa an samu mafita.
Kazalika Yace yasan ababen da yake fadi ( Na tonon silii) wasu basa so, Kuma shi baya tsoron fadin su, akoi ma wasu maganganun na daban da yace ya boye su.

Ya ce idan da shi zai samu shugabancin kasar nan zai kirkiri hukuma wacce zata dinga kula da ma’adanan kasa, sannan ba zai bari ba wani yayi shegantaka a kasar ba.
Sannan Yakuma ce demokoradiya idan babu doka to haukace.
Tabbas idan ana samun masu fitowa ire-iren shi suna haskakawa al’ummar kasa ababen zasu yi sauki.
Su azzalumai a kullum idan suna zalunci basa samun masu kalubalantar zaluncin da suke yi, to za su ci gaba da yi saboda basa samun turjiya. Matukar ana fitowa ana kalubalantar zaluncin da Kuma tona musu asiri zasu saduda sannu a hankali saboda sun san anyi walkiya al’umma sun farka sun ji kuma sun san masu aikata hakan.

Allah ya yi mana mafita, da kariya da sharrin miyagun sarari dana boye.