SHIN KASAN GYARAN DA’AKE SHIRIN YIWA KUNDIN TSARIN MULKIN NIGERIA KARANTA.

Sun Kasa Yiwa Shugaba Buhari Alfarma Su Kuma Suna So Ya Yi Musu.
DAGA Sani BelloBature
Majalissar dattawa da ta wakilan Najeriya sun kasa yiwa shugaba Buhari Alfarmar cire sashe na 84 a kundin tsarin gyaran zabe na shekarar 2022, amma yanzu su kuma suna so ya yi musu.
A kwanakin baya zaran majalissun tarayyar Najeriya sunyiwa shugaba Buhari wayo ya sanya hannu a gyaran sabon kundin gyaran zabe na 2022 inda sashe na 84 ya ce dole me rike da muka wato “appointees” su ajiye mukaminsu wata daya kafin zaben fidda gwani na jam’iyar, inda dokar ta shafi dukanin jam’iu saidai shugaba Buhari ya bukaci a core sashen na 84 inda a karatun farko a zauren majalissar dattawan Najeriya akayi watsi da batun.

Saidai yanzu ƙaiƙai ya koma kan masheƙiya inda yanzu haka ashe a cikin sabon kundin zabe na 2022 ya nuna cewa tun daga kan shugaba kasa, mataimakinsa, gwamna, mataimakin gwamna, sanata, dan majalissar tarayya, ciyaman kansila dukaninsu basu da kuri’a a zaben fitar da gwani na ɗan takarar shugaban kasa, inda yanzu haka “delegates” ne zasu yi zaben wanda yawansu bai wuci dubu biyu ɗari biyar ba.
Shi ne majalissar dattawan Najeriya ta yi maza-maza ta gyara kundin zaben, inda take son shugaba Buhari ya sanya hannu domin basu dama su kada kuri’unsu a zaben fitar da gwani, saidai sun manta da irin tirjiya ta alfarmar da suka sanyawa shugaba Buhari a baya akan sashe na 84 inda yaci wasu mukarraban shugaba Buhari a cikin ministocinsa wanda hakan ya sanya suka janye takararsu saboda basa so su bar mukamansu.
Yanzu dai abinda ake jira a gani shi ne, shin ministan shari’ar Najeriya zai yadda a sanyawa wannan doka hannu bayan waccan sashe na 84 da majalissar taƙi gyarawa ya sanya ya rasa takararsa ta gwaman jihar Kebbi?

Yanzu dai ba a san maci tuwo ba sai miya ta kare.