Labarai

JAMA,A DA YAWA NATA TAMBAYA KANCEWA SHIN OSINBAJO ZAI’IYA… KARIN BAYANI?????

MATAIMAKIN SHUGABAN KASA OSINBAJO ZAI IYA RIKE NIGERIA?

DAGA Datti Assalafiy

Maigirma Mataimakin Shugaban Kasa Professor Yemi Osinbajo yana daga cikin ‘yan takara a jam’iyyar APC da suke neman shugabancin Nigeria da gaske

Kuma Osibanjo yana daga cikin wadanda ake hasashen jam’iyyar APC zata iya tsayar da shi takaran shugaban kasa saboda tasirin da yake da shi a fadar shugaban ƙasa.

Ana hasashen cewa idan APC ta tsayar da Osibanjo, to tsakanin Maigirma Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai da Maigirma Gwamnan jihar Borno @Professor Babaga Zulum wani zai iya zama Mataimakin Shugaban ƙasa.

Kamar yadda a lokuta mu kan auna ‘yan takaran shugabancin kasar Nigeria a mizani na adalci, shima Osibanjo zamu aunashi a mizanin adalci.

Abu na farko Osibanjo yana da ilmi, domin Professor ne, ko magana yake yi idan kana saurara zakaji maganace ta wanda ya goge a fagen ilmi, kuma yawanci jawabin da yake gabatarwa baya rubutasu a takarda, da ka yake zayyano jawabansa

Osinbajo ba matashi bane, kuma ba tsoho bane, yana tsaka-tsaki, yana da lafiyar kwakwalwa da karfin zuciya da zai iya hadiye matsalolin Nigeria ba tare da shakkar tsufa ko kuruciya ba.

Osinbajo bai da tsoro, kuma yana da karfin zuciyar da zai iya taka kowa, da wahala maciya amana su iya juyashi, wanda idan mun dubi yanayin da Kasarnan take ciki to ba shakka Kasar tana bukatar shugaba mai karfin zuciya wanda bai da tsoro wanda zai iya tankwara kowa irin sa.

Osinbajo a shekaru 8 da yayi yana mulkin Nigeria ya kamata ace ya san sirrin Kasar, kuma ya san kura-kuran da suka faru, watakila idan ya zama shugaban Kasa ya iya yin abinda ya dac.

Wannan ra’ayina ne da kuma hasashe, ba lallai ra’ayin mu yazo daya b.

Muna rokon Allah Ya mana zabi mafi alheri ga Kasarmu Nigeria.

arewanahiya

Farin cikinmu shine ganin farin ciki saman fuskarku muna alfahari duku masoya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button