Labarai

YUN KURIN GWAMNATIN JAHAR KADUNA.

Gwamna El Rufa’i Na Shirin Tada Wasu Kauyuka Dake Kan Titin Abuja Zuwa Kaduna

Daga Abubakar A Adam Babankyauta

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El Rufa’i na shirin tada wasu kauyuka dake kan babban titin Abuja zuwa kaduna sakamakon zargin mutanan kauyukan da maba yan ta’addan daji masu garkuwa da mutane bayanan sirri wanda hakan ke haifar da yawan garkuwa da matafiya akan hanyar.

Kamar yadda muka samu labari daga majiyar mu cewa gwamna Nasir El Rufa’i yace da yuwuwar gwamnatin shi zata tashi wasu kauyuka dake kan babban titin Abuja zuwa kaduna sakamakon zargin mutanan kauyukan da tallafawa yan ta’addan daji masu garkuwa da mutane wajen gudanar da harkar ta’addanci akan babban titin.

Kauyukan da El Rufa’i ke tunanin tasa sune Rijana – Kateri – Akilibu wanda gwamnatin shi ke zargin mutanan kauyukan da bama yan ta’addan daji masu garkuwa da mutane bayanan sirri wanda kesa yan ta’addan ke yawan garkuwa da mutane akan babban titin Abuja zuwa kaduna.

arewanahiya

Farin cikinmu shine ganin farin ciki saman fuskarku muna alfahari duku masoya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button