Labarai
GWAMNA TAMBUWAL YAYI BAYANI KAN HALIN DA KASA KE CIKI AHALIN YANZU.

‘Yan Nijeriya Suna Rayuwa Cikin Kunci Da Talauci A Karkashin Mulkin Buhari, Cewar Gwamna Tambuwal
Daga Comr Abba Sani Pantami
Gwamnan Jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal, kuma dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar PDP ya yi zargin cewa ‘yan Najeriya su na rayuwa cikin kunci karkashin mulkin Buhari.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa ya fadi hakan ne yayin da ya gana da wakilan jam’iyyar PDP kasancewar zaben fidda gwanin jam’iyyar ya na ta matsowa.
Ya shawarci ‘yan Najeriya da su kiyaye gwajin shugabanci, su zabi wanda su ka san ya na da gogewar da zai iya dawo da Najeriya cikin yanayi mai kyau.
