Labarai

Ministar kuɗi ta dakatar da Akanta Janar na Najeriya su account fa anshiga tsilla tsilla.

Gwamnatin Najeriya ta dakatar da Akanta Janar na ƙasar Ahmed Idris daga aiki bisa zargin almun da hana da dukiyar kasa har kimanin 80 billions Naira.

Wannan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan hukumar da ke yaƙi da cin hanci da rashawa EFCC ta kama shi bisa zarginsa da almundahana ta naira biliyan 80.

Ministar kuɗi ta Najeriya Zainab Shamsuna Ahmed ce ta dakatar da shi kamar yadda mai ba shugaban Najeriya shawara kan fasahar intanet da kafofin sada zumunta Tolu Ogunlesi ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Ya bayyana cewa dakatar da aka yi wa Ahmed Idris za ta bayar da dama a gudanar da bincike na ƙwarai kan irin zarge-zargen da ake yi masa.

-BBC Hausa

arewanahiya

Farin cikinmu shine ganin farin ciki saman fuskarku muna alfahari duku masoya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button