DA DUMI-DUMI: An kama makiya san zaman lafiyar kasa masu garkuwa da Ɗaliban Jami’ar Greenfield Kaduna.

ALLAH UBANGIJI YA KARA TONA ASIIRIN MARASA SAN ZAMAN LAFIYAR KASAR MU NIGERIA.
Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta sanar da kama Aminu Lawal da Murtala Dawu, wasu masu garkuwa da mutane biyu da ake zargi da kitsa sace daliban jami’ar Greenfield da ke Kaduna a ranar 20 ga Afrilu, 2021.
Muyiwa Adejobi, kakakin rundunar ‘yan sandan ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba.
A cewarsa, mutanen biyun na cikin mutane 31 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban da jami’an rundunar ‘yan sandan farin kaya ta Force Intelligence Bureau Special Tactical Squad (FIB-STS) suka kama.
Hakazalika sun amsa laifin yin garkuwa da daliban jami’ar Greenfield da ke jihar Kaduna, da kuma kashe mutane biyar kafin a biya su kudin fansa, sannan aka sako sauran.
“Jami’an FIB-STS sun kama su a cikin Maris 2022, bayan an ambaci sunayensu cikin masu hannu wajen sace daliban makarantar Bethel Baptist a 2021.”

A ranar 20 ga watan Afrilu ne aka sace daliban jami’ar Greenfield Kaduna, bayan da masu garkuwa da mutane suka kashe uku daga cikinsu.
A yayin harin da aka kai jami’ar mai zaman kanta da ke kan hanyar Kaduna zuwa Abuja, an kuma kashe wani ma’aikacin makarantar.
Daga baya an sake su amma an kashe kusan biyar daga cikinsu yayin da akai garkuwa da su.
Adejobi ya ce za a gurfanar da dukkan wadanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike.
