Labarai

KALLI JAWABIN MALAM IBRAHIM SHEKARAU KAN DALILIN SA NA KOMAWA NNPP.

AHALIN YANZU DAI MALAM IBRAHIM SHEKARAU YA GAR ZAYA ZUWA SABUWAR JAM IYYAR DR RABIU MUSA KWANKWASO WATO NNPP.

KWANKWASO DA SHEKARAU SUN NARKE GURI GUDA A NNPP.

Sanata Mallam Ibrahim Shekarau, Sardaunan Kano, ya karbi katin jam’iyyar NNPP. Haka kuma ya bada sanarwar fita daga jam’iyyar APC.

Bayan ya karbi katin jam’iyyar NNPP, tsohon gwamnan jihar Kano kuma dan takarar shugabancin Najeriya a karkashin tutar jam’iyyar NNPP, Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso, ya mikawa Sanata Shekarau fom na takarar Sanatan Kano ta Tsakiya.

An samu jituwa da amanar yin aikin siyasa a tsakanin Shekarau da Kwankwaso. Babbar manufar haduwar shi ne: a hada karfi da karfe domin a ceto al’ummar Kano da Najeriya daga halin da shiga na rububi da rashin alkibla.

An gaza daidaita sabanin siyasa tsakanin gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje da tawagar ‘yan G7. Duk masu fada aji na Kano a siyasa da sarauta da kasuwanci da harkar addini, sun saka baki, amma lamarin sasancin ya faskara.


Gwamna Ganduje da shugaban masu rinjaye na majalisar tarayya Hon. Alasan Ado Doguwa da mataimakin gwamnan Kano Dr Nasiru Gawuna sun ziyarci Sardaunan Kano har gida, amma ba a daidaita ba. Haka sau biyu, tsohon gwamnan Kano Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso, yana ziyartar Mallam Shekarau har gida, kuma sun fuskanci junansu.

Mallam Ibrahim Shekarau da shi aka kafa APC a 2013, amma shugabancin APC na lokacin da na yanzu suka gaza yin adalci da warware korafi na masalaha don amfanin kowa. Hakan ya tilasta ficewar Sardaunan Kano da hada kai da Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso.

~ Sanata Ibrahim Shekarau

arewanahiya

Farin cikinmu shine ganin farin ciki saman fuskarku muna alfahari duku masoya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button