Labarai

DAYA DAGA CIKIN MASU RUWA DA TSAKI BAN GAREN FIDDA GWANI NA JAM IYYAR APC YAYI KIRA GA SAURAN MASU IKON AKAN HANKAN.

Zaben Shugaban kasar Nigeria nata kara sawo kai sauran jam iyyu sun fitar da dan takarar su inda ahalin yanzu APC ke ko karin fidda nata gwanin.

WANI DELEGATE A KANO YA BUƘACI DELEGATE NA SAURAN JIHOHI SU MARAWA OSIBANJO BAYA A ZAƁEN FIDDA GWANI

Mataimakin shugaban ƙasar Nageriya Farfesa Yemi Osibanjo SAN, ya gana da wakilai masu zaɓe (Delegates) a Jihar Kano domin neman haɗin kai da goyon bayansu a zaɓen fidda gwani na cikin gida na jam’iyyar APC.

A tattaunawar da mu ka yi da ɗaya daga cikin wakilai masu zaɓen (Delegates) wanda ya nemi a sakaye sunansa, ya bayyana cewa gabaɗaya delegate na Jihar Kano sun haɗe kansu Osibanjo za su zaɓa domin sun yaba da nagartarsa da kishinsa ga al’umma.

“Osibanjo shugaba ne irin wanda kowacce al’umma ta ke buƙata domin mutum ne wanda ba shi da ƙabilanci da nuna bambanci, ya ɗauki kowa a matsayin ɗaya musulmai da kiristoci har ma da wanda ba su da addini”. Cewar Delegate.

Haka kuma ya ƙara da cewa ya zama wajibi su yi kira ga duk wasu delegate na kowacce Jiha su haɗa kansu su marawa Osibanjon baya kamar yadda su ka yi a Jihar Kano.

“Ina kira ga ƴan uwana delegate na kowacce Jiha mu haɗa kai waje ɗaya mu zaɓi Osibanjo domin mutum ne wanda in ya samu nasarar zama shugaban ƙasa zai yi ƙoƙari wajen haɗa kan ƴan Nageriya da samar da zaman lafiya gami da ba wa matasa ayyukan yi.

Mun sani cewa Osibanjo bai taɓa munana kalamai kan kowa ba, kuma bai taɓa yin wasu kalamai na nuna tunzuri da tashin hankali ko rarrabuwar kan ƴan ƙasa ba, shi ɗin shugaba ne wanda ya kamata a zaɓa”. Inji Delegate.

ARA,AYIN KA MEYE KAKE GANIN YA DACE?

arewanahiya

Farin cikinmu shine ganin farin ciki saman fuskarku muna alfahari duku masoya.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button