Labarai

GASKIYAR MAGANA KAN CEWA ANKONA GIDAN BISHOP MATHEW KUKAH.

Lafiyata ƙalau, ba a ƙona gidana ba a Sokoto – Bishop Mathew Kukah

Anata cece kuce kan cewa ankona gidan shuganban kiristoci da kansa ya fito ya karyata wan nan magana ba gaskiya bane gidansa na nan lafiya kalau babu abin daya same shi.

Baban malamin Kirista a arewacin Najeriya, Bishop Mathew Kukah na Cocin Sokoto Diocese, ya ce yana nan lafiya ƙalau biyo bayan rahotannin da aka yaɗa cewa an kai masa hari lokacin zanga-zangar da ta ɓarke a Sokoto ranar Asabar.

Bishop Kukah ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa ranar Asabar, yana mai musanta cewa an ƙona gidansa.

Sai dai Kukah ya ce wasu masu zanga-zangar sun kai wa ginin cocin Holy Family Catholic Cathedral hari tare da farfasa gilasai da kuma ƙona wata mota da ke ajiye.

Tuni gwamnatin jihar ta sanya dokar hana fita baki ɗaya bayan arangamar da aka yi tsakanin ‘yan zanga-zanga da jami’an tsaro ta jikkata mutum biyu.

Masu zanga-zangar na neman a saki mutanen da ‘yan sanda suka kama ne kan zargin kisan matashiya Deborah Samuel da suka zarga da zagin Annabi Muhammadu (SAW) ranar Alhamis da ta wuce.

arewanahiya

Farin cikinmu shine ganin farin ciki saman fuskarku muna alfahari duku masoya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button