Labarai

Sheikh Mohammed Bin Zayed Ya Zama Shugaban Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa.

Sheikh Mohammed Bin Zayed Ya Zama Shugaban Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa.

Daga Aliyu A Tsiga

Majalisar ƙoli ta zaɓi Sheikh Mohammed shugaban ƙasa na uku bayan rasuwar ɗan uwansa Sheikh Khalifa bin Zayed. Sheikh Mohamed ya ce ya samu karramawa da amanar da ƴan uwansa suka cusa masa.

An zaɓi Sheikh Mohamed bin Zayed mai mulkin Abu Dhabi a matsayin sabon shugaban ƙasar. Sanarwar a hukumance ta biyo bayan wani taro da sarakunan masarautar suka yi a Abu Dhabi.

Ya zama shugaba na uku a tarihin ƙasar bayan rasuwar Sheikh Khalifa a ranar Juma’a. Kamfanin dillancin labaran ƙasar Wam ya ruwaito matakin da majalisar ƙoli ta tarayya ta ɗauka, wanda ya ƙunshi sarakunan kowace masarautu a faɗin ƙasar.

Sheikh Mohammed ya nuna jin daɗin sa da irin amanar da ƴan uwansa, masu girma da ɗaukaka, ƴan majalisar ƙoli ta tarayya suka damƙa masa, tare da yi masa addu’ar Allah ya taimake shi, ya taimaka masa wajen ɗaukar wannan babban nauyi da kuma cika ta wajen hidimtawa, haɗaɗɗiyar Daular Larabawan da mutanenta masu aminci, a cikin sharhin da jaridar Wam ta ruwaito.

Sheikh Mohammed bin Rashid, mataimakin shugaban ƙasa kuma mai mulkin Dubai, ya taya shi murna. A yau, Majalisar Ƙoli ta Tarayya ta zaɓi ɗan uwana, Sheikh Mohamed bin Zayed Al Nahyan, a matsayin shugaban ƙasar, ya rubuta a shafin sa na Twitter.

Muna taya shi murna, kuma mun yi masa mubaya’a, kuma mutanenmu sun yi masa mubaya’a. Majalisar ta gudanar da taro a fadar Mushrif, wanda Sheikh Mohammed bin Rashid ya jagoranta.

Sheikh Mohammed bin Zayed, Dr Sheikh Sultan bin Muhammad Al Qasimi, Sarkin Sharjah, Sheikh Humaid bin Rashid Al Nuaimi, Sarkin Ajman, Sheikh Hamad bin Mohammed Al Sharqi, Sarkin Fujairah, Sheikh Saud bin Rashid Al Mualla, Sarkin Fujairah, Sheikh Saud bin Rashid Al Mualla. Umm Al Quwain, Sheikh Saud bin Saqr Al Qasimi, Sarkin Ras Al Khaimah sune suka yi zaɓen a zaman da majalisar ƙolin ta gabatar.

arewanahiya

Farin cikinmu shine ganin farin ciki saman fuskarku muna alfahari duku masoya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button