Labarai

SHEIKH DAHIRU BAUCHI YA YI ALLAH WADAI DA ZAGIN MANZON ALLAH SAW DA WATA DALIBA TA YI A SOKOTO.

SHEIKH DAHIRU BAUCHI YA YI ALLAH WADAI DA ZAGIN MANZON ALLAH SAW DA WATA DALIBA TA YI A SOKOTO

…Shehin Malamin Ya yi Kira Ga Sauran Addinai Da su Mutunta Juna Da Kaunan Juna Tare Da Mutunta Annabin Mu Muhammadu S.A.W.

Shahararren Malamin Islama A Najeriya Kuma (Mataimakin Shugaban Masu Fatwa Na Kasa) Sheikh Dahiru Usman Bauchi Yace Duk Wanda Yayi Batanci Ga Fiyayye Halitta Annabi Muhammadu SAW Rayuwarsa Bata Da Amfani. Shehin Malamin Ya Kara Da Cewa Hakan Mummunan Laifi Ne Mafi Muni Wanda Musulmai Baza Su Lamunta Ba.

Sheikh Dahiru Bauchi Daga Karshe Yayi Allah Wadai, Yayi Kuma Kira Ga Dukkan Sauran Addinai Dasu Mutunta Juna Da Kaunan Juna Tare Da Kiyaye Taba Mana Masoyin Mu Wanda Duk Wani Musulmin Duniya Annabi Muhammadu SAW Shine Mafi Kololuwar Abunda Yafi So Duniya Da Lahira.

ALLAH Ya Kawo Mana Karshen Rashin Zaman Lafiya A Najeriya Ya Karawa SHEHU Lafiya Da Daukaka Ya Daukaka Musulunci Da Musulmai Amiiin.

Daga Babangida A. Maina
Tijjaniyya Media News

arewanahiya

Farin cikinmu shine ganin farin ciki saman fuskarku muna alfahari duku masoya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button