Labarai

Dalibai toh afara shirin komawa makaranta.

Dalibai toh afara shirin komawa makaranta.

YANZU-YANZU: Kungiyar Malaman Jami’o’in Najeriya ASUU Na Shirin Janye Yajin Aiki

Wani daya daga cikin yan kungiyar da ya zanta da wakilin jaridar, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce a halin yanzu malaman jami’o’in da ke yajin aikin na tunanin janye yajin aikin na tsawon watanni uku.

Wanda ya janyo cece kuce akafafan Sara Zumunta da kuma kokarin kawo rikici daga daliban jami,ar sassan kasar.

A cewarsa, dakatarwar na iya zama na tsawon watanni uku kacal, yana mai cewa za a ci gaba da tattaunawa da Gwamnatin Tarayya a cikin wa’adin watanni ukun.

Ya ƙara da cewa gazawar gwamnati wajen biyan bukatun ASUU ɗin cikin watanni ukun zai haifar da yajin aikin sai-baba-ta-gani.

Hakan na zuwa ne sa’o’i kaɗan bayan da Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya roƙi ASUU da ta duba halin da ɗalibai ke ciki, ta janye yajin aikin.

Kungiyar ta fara yajin aikin gargadi ne a ranar 14 ga watan Fabrairu saboda gazawar gwamnatin tarayya wajen biyan bukatunta da aiwatar da wasu yarjejeniyoyin da bangarorin biyu suka kulla a baya.

A ranar Litinin 9 ga watan Mayu ne aka tsawaita matakin na masana’antar da wasu makwanni 12, wanda ake sa ran zai wuce ranar 9 ga watan Agusta.

Arewanahiya.com

arewanahiya

Farin cikinmu shine ganin farin ciki saman fuskarku muna alfahari duku masoya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button