Labarai

Yajin aikin ASUU: Buhari ya fadawa ‘daliban Nijeriya “A kara hakuri

Yajin aikin ASUU: Buhari ya fadawa ‘daliban Nijeriya “A kara hakuri”

Shugaban Kasa Muhammad Buhari ya bukaci daliban da ke manyan makarantun gwamnati a Najeriya da su yi hakuri yayin da gwamnati ke kokarin shawo kan matsalolin da ke addabar jami’o’in kasar nan.

Muhammadu Buhari ya kuma yi kira ga kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) da ta duba halin da daliban ke ciki, su janye yajin aikin da suke yi.

Buhari ya yi wannan kiran ne a Ranar Alhamis a bikin ranar samar da albarkatu na kasa karo na 19 da kuma bayar da lambar yabo ta National Productivity Order of Merit Award (NPOM) ga fitattun ‘yan Nijeriya da kungiyoyi 48 a cikin ayyukan gwamnati da na masu zaman kansu, saboda aiki tukuru, da kwazon su.

Shugaba Buhari ya fadi cewa tun da farko ya umarci shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin tarayya, Hon. Ministocin Kwadago da Aiki, Ilimi, Kudi, Kasafin Kudi, da Tsare-Tsare na Kasa da su gaggauta gabatar da dukkan bangarorin kan teburin tattaunawa don sake duba bakin zaren da kungiyar ASUU ke bukata da kuma sauran kungiyoyin kwadago na Jami’a.

©️Arewanahiya.com

arewanahiya

Farin cikinmu shine ganin farin ciki saman fuskarku muna alfahari duku masoya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button