Labarai

Babu Batun Kara Wa Jam’iyyu Wa’adin Zaɓen Fidda Gwanaye, Inji Hukumar Zabe, INEC.

Babu Batun Kara Wa Jam’iyyu Wa’adin Zaɓen Fidda Gwanaye, Inji Hukumar Zabe, INEC

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta nanata matsayin ta cewa ba za ta ƙara wa’adin da ta tsara na gudanar da zaɓuɓɓukan fitar da gwanaye na jam’iyyun siyasa ba.

Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu, shi ne ya bayyana haka a wajen taro karo na biyu da ya kan yi da jam’iyyun siyasa a duk wata hurhuɗu na shekarar 2022, wanda aka yi a ranar Litinin a Abuja.

A cewar sa, akwai ayyuka da dama da masu alaƙa da juna a kan batun wa’adin zaɓuɓɓukan waɗanda tilas ne a aiwatar da su.

Saboda haka, a cewar sa, duk wani canji da za a yi wa wa’adin zai iya shafar sauran ayyukan ta yadda ba a so, kuma yin hakan zai kawo matsaloli ga jam’iyyun da ita kan ta hukumar.

Yakubu ya ce, “Lokacin da jam’iyyun su ka ware domin yin zaɓuɓɓukan fidda gwanayen ya fara ne daga ranar 4 ga Afrilu, 2022 kuma zai ƙare kwanaki 24 daga yau ɗin nan, wato a ranar 3 ga Yuni, 2022.

“Sau biyu a cikin mako biyu da su ka gabata, sai da hukumar ta fito ta tunatar da jam’iyyun siyasa batun muhimmancin da ke akwai na tsayawa sau da ƙafa kan zaɓuɓɓukan su na fidda gwanaye. Ina ƙara nanata matsayin hukumar na cewa ba za a sauya wa’adin da aka tsara ba.

“Akwai ayyuka sosai masu alaƙa da juna waɗanda su ka shafi wa’adin, waɗanda tilas ne a aiwatar da su. Duk wani sauyi da za a yi na ƙara tsawon wa’adin don wani aiki ƙwaya ɗaya zai shafi sauran ayyukan kuma ya jawo matsaloli ga jam’iyyun siyasar da ita kan ta hukumar. A ƙarshe hakan zai haifar da ƙarin manyan matsaloli fiye da abin da aka so magancewa da ƙarin wa’adin.

“Don haka, wannan hukuma ba za ta sauya wa’adin ba. Idan mu ka ci gaba da aiki tare, za mu iya tafiya a kan lokacin wa’adin wajen gudanar da zaɓuɓɓukan fidda gwani cikin aminci da dimokiraɗiyya don zaɓen ‘yan takara na mazaɓu 1,491 waɗanda za a yi wa zaɓe a ranakun 25 ga Fabrairu da 11 ga Maris, 2023.”

Shugaban ya bayyana cewa hukumar tasa ta shirya wani kundi wanda zai zama jagora ga jam’iyyun siyasar wajen gudanar da zaɓuɓɓukan su na fidda gwanaye da fitar da ‘yan takarar zaɓe.

Ya ce: “A bisa tsarin yin aiki tare don bin ƙa’idojin da doka ta tanada, wannan hukuma ta shirya wani kundi da zai yi wa jam’iyyun siyasa jagora wajen gudanar da zaɓuɓɓukan fitar da gwanaye tare da tsayar da ‘yan takarar su na zaɓe, wanda ya haɗa da jerin takardun da ake buƙata don kammala aikin tsayar da ɗan takara cikin nasara.

“Kundin ya na daga cikin ƙunshin takardun da mu ka ba ku na wannan taron. Haka kuma, hukumar ta shirya kalandar lokutan zaɓuɓɓukan fidda gwanaye na muƙaman shugaban ƙasa, gwamna, da majalisun tarayya da jihohi bisa shawarwarin da jam’iyyun siyasa su ka kawo ya zuwa ranar Juma’a, 6 ga Mayu, 2022. Ita ma wannan takarda ta na cikin ƙunshin takardun da mu ka ba ku domin wannan taron.”

Shugaban ya yi kira ga jam’iyyun da su rungumi kowa da kowa wajen gudanar da zaɓe ta hanyar tabbatar da cewa sun ba mata da matasa da naƙasassu damarmaki sosai.

A cewar sa, wannan ce kaɗai hanyar da za su bi su ba jama’ar ƙasa tabbacin sadaukarwar su ga mulki mai nagarta, ba kawai su tsaya a maganar fatar baki ba.

Ya ce: “A yayin da ku ke gudanar da zaɓuɓɓukan fidda gwanayen tare da tsaida ‘yan takarar ku na zaɓe, yanzu ne lokacin da ya dace mu tuna maku sadaukarwar ku ga inganta tafiya tare da kowa da kowa a harkar zaɓe. Mata da matasa da naƙasassu sun jima su na so a riƙa ba su babban wakilci, musamman a muƙaman zaɓe.

“Don tabbatar wa da jama’ar ƙasa cewa ba kawai maganar fatar baki ake yi kan wannan batu ba, ya kamata jam’iyyun siyasa su ƙarfafa wa dukkan waɗanda ba a cika sanya su cikin harkar zaɓe ba gwiwa wajen shiga a dama da su a matsayin ‘yan takara a zaɓe. Wannan kaɗai ce hanyar da za mu bi mu sauya abin da ke faruwa na rashin isasshen wakilci na wannan muhimmin sashe na al’umma, musamnan ma a zaɓaɓɓun majalisu da kuma sha’anin mulki baki ɗayan sa a ƙasar mu.”

Yakubu ya tunatar da masu ruwa da tsaki a zaɓuɓɓukan gwamna da ke tafe a jihohin Ekiti da Osun kan buƙatar da ke akwai ta jam’iyyun siyasa su zo su ga samfur na kayan aikin zaɓen da hukumar ta tanadar masu.

Ya ce, “Idan mun juya ga wasu zaɓuɓɓukan, ina so in tuna maku cewa za a yi zaɓen gwamnan Jihar Ekiti a wata mai zuwa, a ranar Asabar, 18 ga Yuni, 2022, yayin da za a yi zaɓen gwamnan Jihar Osun nan da wata biyu, a ranar Asabar, 16 ga Yuli, 2022.

“Sashe na 42 na Dokar Zaɓe ta 2022 ya buƙaci hukumar da ta gayyato jam’iyyun siyasa domin su duba samfur na kayan aikin zaɓen aƙalla kwana 20 kafin ranar zaɓen. Don kiyaye wannan dokar, mun gayyato dukkan jam’iyyun siyasa da su ke da ‘yan takara a zaɓen gwamnan Jihar Ekiti domin su duba samfur na kayan aikin a ranar Laraba, 18 ga Mayu, 2022 a ɗakin taro na hukumar da ke Abuja da ƙarfe 11:00 na safe.”

Shugaban na INEC ya yi kira ga jam’iyyun da su tabbatar da sun yi yaƙin neman zaɓe mai tsafta ba tare da wata hatsaniya ko tada hankali ba.

Ya ce, “A yayin da ku ke kamnala zaɓuɓɓukan ku na fidda gwanaye tare da shirya wa zaɓuɓɓukan cike gurbi da manyan zaɓuɓɓuka, ina kira a gare ku da ku tabbatar da kun yi yaƙin neman zaɓe mai tsafta ba tare da wata hatsaniya ko tada hankali ba. Don yin hakan, tsayawa kan dimokiraɗiyyar cikin gida ya na da muhimmanci.

“Abin baƙin ciki, yawan ƙararrakin da wasu ‘yan jam’iyya su ka kai junan su kan zaɓuɓɓukan fidda gwani ya zuwa yanzu sun haura 807 da aka samu kafin Babban Zaɓen 2019 inda masu ƙarar su ka maƙalo har da wannan hukuma.

“Bugu da ƙari, duk dai mun san yanayin tsaro da ake ciki a ƙasar nan ya isa babbar matsala. Kada da gangan ko ba da sani ba ku ƙara hargitsa halin da ake ciki ta hanyar halayya ta tashin-tashina ta membobin ku da magoya bayan ku a lokacin zaɓuɓɓukan fidda gwanaye da babban zaɓe.

“A yayin da za mu fara taron mu na biyu daga cikin tarurruka huɗu da za mu yi a bana, ina ba shugabannin jam’iyya tabbacin cewa a yayin da hukuma ba za ta sa hannu a zaɓen ku ba, za dai ta tsaya ƙyam, za mu ci gaba da yin aiki da jam’iyyun siyasa a matsayin su na manyan masu ruwa da tsaki domin alfanun ƙasar mu.

arewanahiya

Farin cikinmu shine ganin farin ciki saman fuskarku muna alfahari duku masoya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button