Labarai

ZANGA ZANGAR DALIBAI DAN NUNA RASHIN AMIN CEWA YAJIN AIKIN ASUU.

Yayan talakawa sun zama ba,abakin komai ba gurin Manyan kasar nan.

Yajin aikin ASUU: Za mu rufe filayen jirgin sama, tituna da wajen zaɓukan fidda-gwani — NANS

Ƙungiyar Ɗalibai ta Ƙasa, NANS ta yi barazanar rufe filayen jirgin sama, manyan tituna da guraren zaɓukan fidda-gwani a ƙasar nan domin nuna rashin jin daɗin ta da ƙarin tsawaita yajin aiki da ASUU ta yi na makonni 12.

A wata sanarwa da Shugaban NANS na ƙasa, Sunday Asefon ya yi a jiya Litinin, ƙungiyar ta yi alla-wadai da abinda ta suffanta da halin ko-in-kula da gwamnatin Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ke yi a kan lamarin.

Shugaban NANS ɗin ya kuma tabbatar da cewa ɗalibai za su yi tsinke a duk guraren zaɓukan fidda-gwani da taruka da jam’iyyu za su yi a ƙarshen watan Mayu.

Tun 12 ga watan Febrairu dai ASUU ta fara yajin aiki, inda lamarin ke ƙara ta’azzara, bayan da ta kasa cimma matsaya da gwamnatin taraiya.

arewanahiya

Farin cikinmu shine ganin farin ciki saman fuskarku muna alfahari duku masoya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button