Labarai

YAN TAKARA 36 NE SUKA SAI FORM MILLION 100.

YANZU-YANZU: ‘Yan Takara 36 Ne Suka Cire Zunzurutun Kudi Har Naira Milyan 100 Suka Sayi Fom Din Takarar Shugaban Kasa, Mutane 109 Ne Suka Sayi Na Gwamna A Naira Milyan 50

Daga Comr Abba Sani Pantami

Mutane 270 suka sayi na dan majalisar Dattijai, inda mutane 969 suka sayi na dan majalisar Tarayya.

Haka zalika kusan mutane sama da 2,000 ne suka sayi na majalisar dokokin jihohin Najeriya.

Sakataren tsare tsaren Jam’iyyar APC na kasa Alh. Sule Argungum ne ya shaidawa manema labarai adadin yawan mutanen da suka sayi Form domin neman kujeru a jam’iyyar APC.

A yau Talata jam’iyyar za ta rufe saida fom din ta, inda ‘yan takarkari suke ta maida fom din su a halin yanzu bayan sun cike.

arewanahiya

Farin cikinmu shine ganin farin ciki saman fuskarku muna alfahari duku masoya.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button