Labarai

‘YAN JARI HUJJA NA YIN ABINDA SUKA GA DAMA A NIGERIA.

‘YAN JARI HUJJA NA YIN ABINDA SUKA GA DAMA A NIGERIA

DAGA Datti Assalafiy

Wannan shine Gwamnan Babban bankin Nigeria Godwin Emefiele, tsohon shugaban Kasa Jonathan ya kawoshi a ranar 6-3-2014 bayan ya kori tsohon Gwamnan Bankin Sunusi Lamido Sunusi.

Da shugaba Muhammadu Buhari yazo a 2015 madadin ya koreshi ya kawo amintaccensa sai ya kyaleshi.

Godwin Emefiele yazo ya tarar da darajar Naira ana canzata da kudin Dalar Amurka daya bai kai Naira 200 ba, amma yau ana canza Naira daya da Dalar Amurka 580 a bakar kasuwa.

Godwin Emefiele shine ke dauke da alhakkin karya darajar kudin mu Nigeria a duniya, kuma ba zai taba tsallake zargi da tuhuma akan karyewar tattalin arzikin Nigeria ba.

Me yasa Godwin Emefiele ya kawo wannan lokacin Buhari bai koreshi ba har ma ya kara masa wa’adin shekara 5? dalili shine, akwai wasu manyan maciya amana da suke jikin shugaba Buhari, sune uwayen gidan Godwin Emefiele, duk abinda suke so suyi da kudi to ba sai ance komai ba, yaron su ne, suna jin dadinsa, su suka hana a sallameshi.

Abin mamaki, wai wannan mutumin shima ya sayi fom din tsayawa takaran shugaban Kasa a Jam’iyyar APC, kuma yaki ya sauka daga kujerarsa na Gwamnan Babban Bankin Nigeria, harma ya ruga Kotu domin ya samu kariya, wato a lokaci guda yana takaran shugaban kasa kuma yana Gwamnan Babban Banki saboda yana da masu daure masa gindi a jikin Baba Buhari.

Ina fatan a samu canjin Gwamnati, a kawo wanda zai tsananta bincike mai karfi akan mukarraban shugaba Buhari, domin kamar yadda Sheikh Bello Yabo ya fada, ba’a taba Gwamnatin da akayi wasa da dukiyar kasa kamar wannan Gwamnatin na Baba Buhari ba, akwai kamshin gaskiya a maganar Malam.

Allah Ka ceci Nigeria.

arewanahiya

Farin cikinmu shine ganin farin ciki saman fuskarku muna alfahari duku masoya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button