Labarai

SANARWAR HUKUMAR ZABE GA MASU TAKARA.

HUKUMAR ZABE MAI ZAMAN KANTA TA FITAR DA SANARWA GA DUKKAN JAM,IYYU MASU TAKARA.

ZABEN 2023: INEC Ta Kayyade Wa Jam’iyyu Wa’adin Kammala Zaɓuɓɓukan Fidda Gwani

HUKUMAR Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta gargaɗi jam’iyyun siyasa da su tabbatar da cewa sun kiyaye jadawalin gudanar da zaɓuɓɓukan su na fidda gwani na manyan zaɓuɓɓukan shekarar 2023.

Babban Kwamishina kuma Shugaban Kwamitin Yaɗa Labarai da Wayar da kan Masu Zaɓe na hukumar, Mista Festus Okoye, shi ne ya bada wannan gargaɗin cikin wata sanarwa a ranar Alhamis.

Okoye ya tunatar da cewa a ranar 26 ga Fabrairu, 2022, hukumar ta fitar da Jadawali da Tsarin Ayyuka na Manyan Zaɓuɓɓukan 2023, inda ta tanadar wa jam’iyyun da cewar su gudanar da zaɓuɓɓukan fidda gwanayen su don tsaida ‘yan takara daga ranar 4 ga Afrilu zuwa 3 ga Yuni, 2022.

Wannan na nufin cewa hukumar ba za ta amince da duk wani zaɓen fidda gwani da aka yi bayan wa’adin ya cika ba.

Kwamishinan ya ce: “Domin kiyaye sashe na 82(1) na Dokar Zaɓe ta 2022, dukkan jam’iyyun siyasa 18 sun bada sanarwar da ake buƙata da ke nuna ranakun da za su yi manyan tarurrukan su na ƙasa, da zaɓuɓɓukan fidda gwani domin tsayar da ‘yan takarar muƙamai daban-daban kamar yadda aka zayyana a Tsarin Mulki da Dokar Zaɓe.

“Wasu daga cikin jam’iyyun har sun fara aikin, wanda ya sa hukumar ta tura ma’aikata domin su sa ido kan yadda ake ayyukan kamar yadda doka ta buƙace ta ta yi.

“Saboda ganin muhimmancin aikin wajen samar da ‘yan takarar muƙamai daban-daban na zaɓe a Manyan Zaɓuɓɓukan 2023, ya na da muhimmanci a tunatar da jam’iyyun siyasa cewa ya rage masu wata ɗaya daga yau su kammala zaɓuɓɓukan su na fidda gwani.

“Wa’adin ƙarshe dai shi ne ranar Juma’a, 3 ga Yuni, 2022. Yayin da ta ke kira ga jam’iyyun da su tabbatar da sun yi zaɓe babu wata hatsaniya, kuma fisabillahi, hukumar ta na nanata cewa wa’adin na nan daram daƙam babu canzawa.”

Okoye ya kuma ce ana so a miƙa sunayen ‘yan takarar zaɓen Shugaban Ƙasa da Majalisar Tarayya ne ta hanyar gidan yanar INEC daga ranar 10 zuwa 17 ga Yuni, yayin da za a miƙa sunayen ‘yan takarar gwamna da majalisun dokokin jihohi daga ranar 1 zuwa 15 ga Yuli.

“Ana ƙara tunatar da jam’iyyun siyasa cewa tilas ne sunayen ‘yan takarar da za su miƙa wa hukumar su kasance waɗanda aka samar ne ta hanyar zaɓen fidda gwani da aka yi fisabilillahi.”

Okoye ya ce hukumar za ta ci gaba da yin aiki tare da jam’iyyun siyasar don tabbatar da an kiyaye Tsarin Mulki da Dokar Zaɓe da jadawalin dukkan ayyukan da aka tsara yi a cikin Jadawali da Tsarin Ayyukan Manyan Zaɓuɓɓukan 2023.

arewanahiya

Farin cikinmu shine ganin farin ciki saman fuskarku muna alfahari duku masoya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button