Labarai

LABARI DA DUMI DUMI: Barayi sun shiga babban bankin kasa na Abuja.

LABARI DA DUMI DUMI: Barayi sun shiga babban bankin kasa na Abuja

Daga Barrista Nuraddeen Isma’eel

“Tun a bayan da akaji wata sanarwa, dake nuni da cewa, Shugaban bankin Nijeriya Godwin Emefile zai tsaya takarar Shugabaancin Nijeriya!

“Hakan yana da nasabar yadda aka ga wasu kungiyoyin matasa mazauna Abuja, sun fito cikar su da kwarkwatun su suna zanga-zangar kira ga shi Shugaban bankin daya fito takarar Shugaban kasa a zaben kakan bana mai zuwa ta 2023.

Jaridar 9News Nigeria ta ruwaito cewa, Godwin Emefile a ranar juma’ar data gabata, ya bada sanarwa a cikin wani faiain bidiyo na fitar da kudi, Wanda suka tabbatar da iya adadin kudin siyan fam ne na tsayawa takarar Shugaban kasa karkashin inuwar jami’yyar APC kan Naira Miliyan 100.

“Har wala yau dai a ranar ne; Sai aka ga wasu mutane rufe da fuskokin su, dauke da bindigu sun nufo babban bankin kasa, basu tsaya ko’ina ba Sai gaban Shugaban babban bankin kasan a domin ya amince da saka hannu don fitar da wasu kudade kamar yadda fai-fan wani bidiyo ya nuna haka, kuma babban kamfanin dillancin labarai na 9News Nigeria ya tabbatar da hakan.”

“Sai dai an tabbatar cewa, halartan wadannan miyagun na zuwa babban bankin kasa dauke da bindigu, yana da nasabar sanarwan da shugaban babban bankin wato Godwin yayi, na shirye-shiryen siyan fam din tsayawa takarar Shugaban kasa karkashin inuwar jam’iyyar APC, Amma majiyar ya tabbatar cewa! Shugaban babban bankin kasan ya tattara wadannan kudaden na sayen fam din daga babban bankin kasan tun a ranar Alhamis din.”

Bisani sai aka ga barayin sun fito sunata mazurai, sannan suka shiga motar su suka yi gaba, ammafa basu tafi dako sisi daga babban bankin Nijeriyan dake birnin tarayya Abuja.”

arewanahiya

Farin cikinmu shine ganin farin ciki saman fuskarku muna alfahari duku masoya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button