Labarai

HATSARIN JIRGIN RUWA YAYI SANA DIYYAR RASUWAR MUTUN SHA BIYAR A KATSINA.

Allahu Akbar Allah mai yadda yaso da bawan sa Allah Ubangiji ya jikan wadan da suka rasu Rayuwa babu tabbas kullu nafsin za,ikatul maut.

An Yi Jana’Izar Mutane Sha Biyar Da Suka Rasu A Hadarin Jirgin Ruwa A Katsina

Maigirma Kwamanshinan Ma’aikatar kula da Ayyukan Kananun Hukumomi da Masarautu na Jihar Katsina Rt, Hon Ya’u Umar Gwajo’Gwajo ya halarci jana’izar mutane sha biyar da suka rasu a hadarin jirgin ruwa (KWALE KWALE) a Dam din Sabkedake karamar Hukumar Mai’adua.

A jiya da dare ne aka samu wannan hadari na kifewar jirgin wanda aka yi asarar rayuwaka sha biyar, inda aka gudanar da jana’izarsu yau da safe 7:30 a garin Tsabu dake karamar hukumar Mai’adua.

Hon Gwajo’Gwajo wanda na daga cikin wadanda suka samu halartar jana’izar ya bayar da tallafin naira dubu dari da hamsin tare da buhun masara shida nan take domin bayar da sadaka ga iyalan mamatan.

Muna Fatan Allah ya jikansu ya gafarta masu Allah ya kyautata karshenmu idan ya zo.

Daga Saddam Umar Akama Shirwa

arewanahiya

Farin cikinmu shine ganin farin ciki saman fuskarku muna alfahari duku masoya.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button