Littafan Hausa Audio

KALAMAI MASU SANYA BUDURWA FARIN CIKI MARA ADADI.

Masana Soyayya Sunyi Sharhi akan Iya Magana Tabbas Na daya daga cikin abubuwa masu hada soyayya takara karko azuciyar masoya.

Domin ita mace burinta farin ciki akowanne lokaci haka tana bukatar lallashi da kuma tarairaya daga gurin abun da take so.

Furta Mata Wadannan Kalmomin Kaga Yadda Zaka Rikita Ta Saboda Dadi:

SHARE ?
#Tsangayarmalamtonga

Kalamai karama zaka fadawa mace ya sata farin ciki. Kana Iya fada mata wani gungumemen kalma kuma ka bata mata rai.

Furtasu, lokacin furtasu, da kuma yanayin furta sune matsalar akasarin maza. Haka yasa kalaman da suke furtawa matansu ko ‘yan matansu basa musu tasiri.

Ga wasu kalmomin da lokacin furta su da ya kamata duk namiji ya sansu.

1: Duk mace tana son ka zuga muryarta. Nuna mata misalin yadda zakin muryarta yake saka shauki, ya sa aka haramta bayyana sautin mace.
Wannan kalmar zuga yana da tasiri ne musamman ga macen da baku taba haduwa ba.

Idan kuma wacce kuka taba haduwa ce ko matarka ce. Sanar da ita yadda sautin muryarta yake saka samun natsuwa da kwanciyar hankali.
Mata suna son a zuga muryarsu kamai rashin dadin sautin nata kuwa.

2: Mata suna son ka Yaba gashin kansu.
Duk wata mace gashin kanta abun alfaharinta ne.
Don haka a duk lokacinda ka kaita gyaran gashi ta salon, ko tayi sabon kitso, koma ta tsaife shi. Shafa mata shi. Yi mata wasa dashi. Zuga mata shi na yadda ya dace da kanta. Sumbace shi.

Duk namijin da yake yawan yiwa matarsa wadannan abubuwan da gashin kanta sai rika shiga ranta.
Mata sun tsani suyi gyaran gashi ko kitso namiji yayi burus kamar bai gani ba.

3: Ba telanta zaka soma zugawa ba, ko yadda kayan suka mata kyau ba. Kiran jikinta shi zaka yaba ka kuma nuna mata telolinta kawai kudinta suke ci amma baiwa da Allah (SWT) Ya mata sune suke dacewa da duk wani suturan data saka.
Tabbatar mata hakan ta nuna mata yadda kuma kyanta ke fin hakan fitowa idan tayi shiga na kayan Turai dinkanku.

Mata suna son wannan suga koda kuwa ragga ne a jikinta.

4: Tabbatar mata irin baiwa da basiran datake dashi ba duk mata ake samunsu da su ba.
‘Yan mata suna son wanda ya nuna yana sonsu ya tabbatar musu sunada wani abu na musamman na baiwa da ba a samunsu a wajen kowace irin mace.

5: Idan a ranar ka soma ganinta gaba da gaba ko hotunanta. Siffanta ta da wasu jinsin mata mafi kyau a duniya.

Nuna mata koda dai baka sani ba, kasan wannan kyau daga wajen Hajiya ma’ana uwarta ta samushi.

Tabbatar mata tana da alaka da Larabawa saboda kyaun siffanta ko Fulani. Idan ta sanar da kai kabilanta. Nuna mata sam taje ta tambaya tanada nasaba da wasu jinsin da aka sansu da kyau.

Mace komai muninta tana son mai sonta ya tabbatar mata tafi sauran mata kyau a idanuwansa.

6: Duk mace tana so ka nuna mata ka yaba da natsuwarta, hankalinta da dabi’unta.
Idan wannan ne haduwarku na farko ko kuma mu’amalar ku ko ta charting ne. Nuna mata duk da bakasan mahaifinta ba kasan wadanna kyawawan abubuwan daka lissafosu daga wajen mahaifinta ta dauko su.

7: Nuna mata zaka so ace ka rabata da duk wasu masu sonta da zaka gano sirrin da zaka bi ka mallaketa. Idan ka samu shiga zata ce maka ai batada samari ko kuma ta nuna maka ko furta maka wani abunda zaka mata na sace soyayar ta cikin raha kamar yadda zaka mata bayanin cikin raha.

Mata suna son namiji ya nuna musu a shirye yake a yi duk abunda zai iya yiwuwa domin samun soyayyar su.

8: Zuga irin girkin data maka idan matarka ce. Yaba da abunda ta kawo maka daga gidansu koda ruwan sha ne idan budurwar kace.
Nuna mata yadda baka sha’awar cin abinci a waje idan ka tuna babu irin girkin da matarka bata iya ba.

Nuna mata yadda kake jin dadin yadda take miko maka abunda ta kawo maka idan budurwar kace.

9: Sanar da ita irin rokon Allah da kayi kamin kayi dacen aurenta. Ko haduwa da ita idan budurwar kace.
Tabbatar mata ita zabine na Allah a gareka bana son rai ba.

10: Furta mata burinka kayi rayuwa da ita na har abada.
Mace idan tana sonka ko tana aurenka bata tunanin akwai ranar da zaku rabu. Tabbatar mata da hakan taji daga bakinka hakan zai kara mata shaukin amincewa da kai.

Da fatan maza zasu daure su rika furtawa matansu kalamai masu dadi da zai yi tasiri a zukatansu.

arewanahiya

Farin cikinmu shine ganin farin ciki saman fuskarku muna alfahari duku masoya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button