SHAHARARREN DAN KASUWAR NAN NA JAHAR KANO DAN ASALIN KASAR LABNON.

Fitaccen ɗan Kasuwar nan na Kano Tahir-Fadlallah ɗan asalin ƙasa Labanon, kuma mamallakin Otal ɗin Tahir Guest Palace ya rasu, yana da shekaru 74 a Duniya.

Mai magana da yawun shugaban ƙasa Malam Garba Shehu ne ya bayyana hakan ta shafinsa na Facebook.

Kafin rasuwarsa shi ne Shugaban ƴan ƙasar Labanon mazauna Kani.

Kawo yanzu dai babu ƙarin bayani game da rasuwar tasa.

Sai dai tuni jama’a suka shiga bayyana alhini a kafafen sada zumunta.

Sai ku biyo mu nan gaba domin ci gaban wannan kabarin.

– Freedom Radio

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button