Shugaban KCPC, Idris Dambazau ya tsere daga hannun jami’an hukumar yaƙi da Cin-hanci ta Kano

Shugaban KCPC, Idris Dambazau ya tsere daga hannun jami’an hukumar yaƙi da Cin-hanci ta Kano

Yayin da ya ke fuskantar tuhume-tuhume a Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe da Cin-hanci da Rashawa ta Jihar Kano, PCACC, bisa zargin cin-hanci, Shugaban Hukumar Kula da Hakkin mai Saye ta Jihar Kano, Idris Bello Dambazau ya tsere da ga hannun jami’an PCACC.

Shugaban PCACC, Barista Mahmoud Balarabe ne ya baiyana hakan a yayin ganawa da manema labarai.

Ya ce, shashin aikace-aikace na hukumar su na tsaka da yi wa Dambazau ɗin tambayoyi na tsawon awanni, sai ya bada uzirin a bar shi ya je gida ya sha magungunan sa da ya saba sha a kullum.

A cewar Balarabe, jami’an sa ne su ka kira shi bayan ya bar ofis, su ka shaida masa uzurin na Dambazau, in da ya ƙara da cewa “Ni kuma sai na basu izinin su raka shi gidan nasa ya sha magungunan saboda harkar lafiya ba a wasa da ita”.

Shugaban PCACC ɗin na riƙo ya ƙara da cewa ko da jami’an sashin aikace-aikacen su ka raka Dambazau ɗin gida, kawai sai ya tsere.

Ya ce kuma akwai Ƙorafe-ƙorafe masu yawa na zargin cin hanci a kan Dambazau, dalilin da ya sa hukumar ta gaiyace shi ya zo ya kare kan sa, amma ya ƙi zuwa sai jiya Talata bayan an aika masa takardar gayyatar da dama yaƙi zuwa, har sai da hukumar tai barazanar kamo shi.

Balarabe ya ce ko da a ke tuhumar Dambazau, bai bada wasu gamsassun amsoshi ba, inda ya ƙara da cewa tserewar da yayi ya kara wa kan sa laifin kumar hukumar za ta yi abinda ya dace, bisa doka a kan sa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button