Labarai

GWAMNATIN TARAYYA TA KADDAMAR DA DOKA AKAN MASU BIYAN KUDIN FANSA.

Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da dokar hukunta duk wanda aka samu ya biya kudin fansawa masu garkuwa da mutane.

Za a fara ɗaure waɗanda su ka biya kuɗin fansar ƴan uwansu da a kai garkuwa da su

Majalisar Dattijan Nijeriya ta zartar da wani ƙuduri da zai tabbatar da hukuncin ɗaurin aƙalla shekara goma sha biyar ga masu biyan kuɗin fansa don kuɓutar da wani da aka sace.

BBC Hausa ta rawaito cewa ƙudurin dokar ya kuma amince da hukuncin kisa ko daurin rai-da-rai a gidan yari ga duk wanda aka samu da laifin satar mutane.

Ƙudurin, wanda gyaran fuska ne ga dokar yaƙi da ta’addanci, ya ƙunshi ɗaurin rai-da-rai ga masu satar mutanen da kotu ta kama da laifi, kuma matukar satar ta kai ga mutuwar mutum, masu laifin za su fuskanci hukuncin kisa.

Bangaren da ke cike da ka-ce-na-ce a ƙudurin dokar dai shi ne wanda ya nemi ɗaure duk wani mutumin da ya biya kuɗin fansa ga masu satar mutane.

arewanahiya

Farin cikinmu shine ganin farin ciki saman fuskarku muna alfahari duku masoya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button