BATUN SABON SHUGABAN JAM,IYYAR APC.
DA DUMI-DUMI: Sabon shugaban jam’iyyar APC Sen. Abdullahi Adamu ya ce duk wanda ba zai iya siyan Form ɗin tsayawa takarar shugaban kasa miliyan ɗari ba to bai chanchanci zama shugaban ƙasa ba.
Shugaban ya jaddada cewa APC itace babbar Jam’iyya a yanzu wacce kowa yake son shiga don haka dole form dinta yayi tsada.
Ya sake bayyana cewa duk wanda ba zai iya ba ko magoya bayansa ba zasu iya ba to dan tasha ne mara amfani har ya misalta hakan da kare a cewarsa.
Najeriya pha ba wai jiharku ba, ko sarauta za’a maka ai ka biya miliyan ɗari ba neman shugabancin Najeriya ba.
Shugaban ya bayyana cewa miliyan ashirin ya biya saboda ya sayi form ɗin tsayawa takarar shugabancin jam’iyyar wanda a baya dubu dari biyar ne don haka dole duk mai so ya biya abinda aka gindaya.
Daga Comr Haidar Hasheem Kano