Shugaba Buhari Ya Fi Shugabannin Baya Aiki A Ƙasar Nan, Inji Walin Kazaure.

Shugaba Buhari Ya Fi Shugabannin Baya Aiki A Ƙasar Nan, Inji Walin Kazaure

Tsohon Babban Sakataren Ma’aikatar Ayyuka da Gidaje ta Ƙasa, Alhaji Babangida Husaini ya bayyana cewa shugaban ƙasa mai ci, Muhammadu Buhari ya fi shugabannin ƙasa da su ka shuɗe yin aiki.

Husaini, wanda kuma shi ne Walin Kazaure, ya bayyana hakan ne lokacin da ya ke ganawa da manema labarai a mahaifarsa ta Kazaure dake Jihar Jigawa a yau Talata.

Yace idan a ka yi la’akari da manyan ayyukan hanyoyin sufuri a kasar nan, babu shakka za’a yaba wa Gwamnatin ta Buhari.

” Mafi yawancin Tituna da su ka haɗa jihohin kasar nan sun daɗe su na cikin wani hali, amma da zuwan Gwamnatin ta Buhari kusan kashi 90 na ayyukan sun kammalu,” in ji shi.

Walin Kazaure ya ƙara da cewar a bangaren hanyoyin sufurin jiragen ƙasa, babu shakka ya kamata a yaba wa gwamnatin ta Buhari duba da yadda ta himmatu wajen kawo sabbin jirage da kuma zamanantar da sha’anin sufurin, sannan ga kuma ayyukan da suka shafi Noma,samar da ayyukanyi ga matasa da dai sauran ayyuka daban daban.

Alhaji Balarabe Husaini wanda ke neman kujerar Majalisar Dattijai daga Yankin Jigawa ta kudu, ya buƙaci al’ummar kasar nan da su ci gaba da bawa jam’iyyar APC hadin kai domin samun nasarar kakar zaben 2023.

Shin ko kun yadda da wanga batu ?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button