Labarai

GWAMNA AMINU WAZIRI TAMBUWAL ZAI KOMA APC.

YANZU-YANZU: GWAMNAN JIHAR SOKOTO AMINU WAZIRI TAMBUWAL NA SHIRIN DAWOWA JAM’IYYAR APC

Buhari Ya Yi Ganawar Sirri Da Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa Na Jam’iyyar PDP, Gwamna Tambuwal Na Jihar Sokoto

Fadar shugaban ƙasa ta ce, shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da gwamnan Sokoto Aminu Tambuwal sun gana a fadar shugaban ƙasa dake Abuja.

Tambuwal dai na ɗaya daga cikin masu neman tikitin takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar adawa ta PDP.

Ganawar da Buhari na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan shirin yarjejeniyar jam’iyyar PDP da aka tsara na ƴan takarar shugaban ƙasa huɗu a Arewa ya faɗa cikin ruɗani.

Wasu na ganin gwamna Aminu Waziri Tambuwal na iya dawowa Jam’iyyar APC idan an cimma matsaya.

Me za ku ce ?

arewanahiya

Farin cikinmu shine ganin farin ciki saman fuskarku muna alfahari duku masoya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button