Labarai

LABARI DA DUMI DUMINSA.

DA DUMI DUMINSA: Gwamnatin Tarayya Zata Bada Tallalfin Kayan Abinci Ga Marassa Karfi

 

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da a gaggauta sakin metirik tan 40,000 na hatsi daga asusun ajiyar abinci domin taimakawa marasa galihu a Najeriya wajen gudanar da bukukuwan Easter da Sallah masu zuwa.

 

Ministan Noma da Raya Karkara, Muhammed Mahmood ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai na fadar gwamnati bayan ganawar sirri da Buhari a fadar shugaban kasa da ke Abuja ranar Talata.

 

Mista Mahmood, ya ce shugaban kasar ne ya gayyace shi tare da umarta ta da ya raba kayayyakin ga mutanen da abin ya shafa, ya kuma bayyana fatansa na cewa atisayen zai kuma rage illar hauhawar farashin hatsi a kasuwa.

 

A cewarsa, tan 12,000 daga cikin tan 40,000 da aka amince da su, za a baiwa ma’aikatar kula da jin kai da bala’o’i da ci gaban jama’a ta tarayya domin rabawa ga ‘yan gudun hijira a fadin kasar nan.

 

“Na zo nan da yammacin yau ne sakamakon sammacin da shugaban kasa ya yi masa.

 

“Ya ba da umarnin kuma ya amince da fitar da hatsi daga Ma’aikatar Aikin Gona da Raya Karkara ta Tarayya,” in ji Mista Mahmood yana cewa.

 

“Wannan shi ne don rage tasirin wasu matsalolin da muke fuskanta na hauhawar farashin kayayyaki a fadin kasar nan.

 

“Don a sanya hatsi yayi araha ga mutane don yin bukukuwan – Ramadan, Ista da kuma Sallah.

 

“Za mu kuma ba da wasu hatsi ga ma’aikatar jin kai, don yin rabon.

 

“Hatsin yana fitowa ne daga Tsarin Hatsi namu kamar yadda Shugaba ya umarta,” “in ji shi.

 

Ministan ya bayyana cewa irin tsarin da aka yi amfani da shi a lokacin kulle na cutar COVID-19 a shekarar 2020, don raba tan 70,000 na abinci iri daban daban a wasu jihohi kuma za a yi amfani da Babban Birnin Tarayya wajen rarraba hatsin.

 

“Idan zaku iya tunawa ayayin barkewar cutar ta COVID, Shugaba Buhari ya kuma ba da umarnin kuma ya amince da sakin hatsi.”

 

_Majiya Jaridar #NAN

arewanahiya

Farin cikinmu shine ganin farin ciki saman fuskarku muna alfahari duku masoya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button