SENATOR BARAU I JIBRIN MALIYA.

SANATA BARAU I JIBRIN MALIYA, YAMIƘA SAƘON GODIYA GA MAI GIRMA SHUGABAN ƘASA MUHAMMAD BUHARI, BISA AMINCEWA DAYAYI NA GINA MAKARANTAR FASAHA TA TARAIYAR NAJERIYA A ƘARAMAR HUKUMAR KABO DAKE YANKIN SA NA KANO TA AREWA.
Mai girma zaɓaɓɓen sanatan kano ta arewa Barau I. Jibrin Maliya, cikin girmamawa yana miƙa saƙon godiya ga Mai girma Shugaban Ƙasa Muhammad Buhari, bisa bada umarnin ginin makarantar Federal Polytechnic, Kabo a jihar Kano.
A matsayina na Sanata mai wakiltar Kano ta arewa shiyyar da aka bada umarnin kafa wannan makaranta, Ni da Al’ummar wannan yanki namu baki ɗaya na Kano ta arewa, muna miƙa saƙon godiya mara misaltuwa ga mai girma Shugaban Ƙasa Muhammad Buhari, bisa kawo wannan aiki mai ɗunbin alkairi tare da albarka da muhimmanci mara misaltuwa yankin mu.
Ilmi shine ƙashin bayan cigaban dukkanin wata Al’umma, wannan na ɗaya daga cikin manyan dalilan da suka sa Shugaban ƙasa ya maida hankali wajen ƙirƙiro manyan makarantun gaba da sakandare a dukkanin jihohin ƙasar nan baki ɗaya, nima shine babban dalilina na dayasa na kai ƙuduri domin ganin an gina makarantar federal Polytechnic Kabo a yankin da nike wakilta na Kano ta arewa anan Kano.
Ina godiya ga shugaban Ƙasa bisa amsar buƙatar mutanen yankina na ƙudurin dana gabatar har yakai gareshi.
Ina godiya ga ministan ilimi na Najeriya Malam Adamu Adamu, bisa ƙoƙarin sa da haɗin kansa na ganin wannan aiki ya yiwu.
Dukkanin Mutanen yankin Kano ta arewa jihar Kano dama ƙasa baki ɗaya na godiya, Shugaban Ƙasa Muhammad Buhari.
Nagode
Mai girma zaɓaɓɓen sanatan kano ta arewa Barau I Jibrin Maliya.