Labarai

BABBAR MAGANA.

DA DUMI DUMINSA: Shugaban Jam’iyar APC Na Kasa Abdullahi Adamu Yayi Murabus Daga Kujeran Sanata.

Wani sai babbar kasar mu ta nageria kana wani mataki babban burin ka shine zuwa mataki na gaba.

Daga Muhammad Kwairi Waziri

Sabon Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya ajiye kujerarsa ta dan Majalisar Dattawa.

A safiyar Talata ne Sanata Abdullahi Adamu ya sanar da Majalisar cewa ya sauka daga kujerar dan Majalisar Dattawa Mai Wakilatar Nasarawa ta Yamma.

Hakan na kunshe ne a takardar ajiye aiki da ya aike wa Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan a ranar Talata, mako biyu da zamansa shugaban jam’iyyar APC mai mulki.

A zaman Majalisar ta ranar Talata shi ma Mataimakin Shugaban Jam’iyar APC na Kasa Mai Wakiltar Yankin Arewa, Sanata, Abubakar Kyari ya mika takardarsa ta saukarsa daga kujerar dan majalisa mai wakiltar Borno ta Arewa.

’Yan majalisar su biyu, su dauki matakin ne bayan zamansa Shugaban Jam’iyyar APC mai mulki, wanda aka zabe shi a babban taron jam’iyyar na ranar 26 ga watan Maris.

Tun bayan darewar jiga-jigan ’yan siyasar a kan kujerar jagorancin jam’iyyarsu ake ta ce-ce-ku-ce game da halascin ci gaban da zamansu a matsayin ’yan majalisa da kuma shugabannin jam’iyya.

A kan haka ne dai wasu ke ta ce sai dai su hakura da kujerunsu ta Majalisar Datttawa.

Yanzu dai Borno ta Arewa, wadda Sanata Abubakar Kyari ya wakilta da Nasarawa ta Yamma, wadda Abdullahi Adamu za su kasance ba su da wakilai a Majalisar Dattawa.

Abin da ya rage gaba, shi ne majalisar ta sanar da Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) game da gibin da aka samu a wadannan mazabu domin hukumar ta shirya gudanar da zaben cike gurbi a nan gaba.

Babban burin yan kasa yanzu she Allah ubangiji ya taimaki mu ya bamu Shuwa gabannin nagari masu jin tausayin talakawa.

arewanahiya

Farin cikinmu shine ganin farin ciki saman fuskarku muna alfahari duku masoya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button