ALLAH GATAN BAWA.

Akwai tausayi da radadin zafin bacin rai yayin da duk wani mai imani zai yi arba da wa ‘yan nan ‘yan gudun hijirar a cikin watan Ramadan.

Wallahi sai ka ce babu gwamnati da shugabanni masu madafun iko a kasar.

Zuciya ta, tayi matukar kaduwa a lokacin da na ci karo da wannan hoton.

Wallahi musani kamar yadda muke suma haka suke, babu wani bambanci a tsakanin mu da su, amma yau jindadi da walwala a garuruwan su ya gagare su.

Tabbas duk wani jin dadi bai wuce samun lafiya ba, tare da zama a cikin iyalanka, garinka, kaci ka sha san nan kuma ka tufatar da Su Hakan Shine Farin cikin duk wani mai iyali.

Yayin da mu muke cikin walwala su acikin kunci suke, ba su iyaci Sha balle har su koshi.

A cikin wannan azumin watan Ramadan mai Albarka da ake bukatan kowane Musulmi ya samu nutsuwa, domin gudanar da ibada mai kyau, amma su suna chan suna ta fama da zafin rana da yunwa da rashin kwanciyar hankali.

Wallahi duk shugaban da ya gagara kare hakkin al-ummar shi, to wallahi kada ma ya yadda ya mutu har ya koma ga Ubangiji, domin wallahi ba zaiga mai kyau ba.

Muna Addu’ar Allah ya kawo mana karshen wannan bala’in da muke fama dashi a yankin mu na Arewa, dama kasar Najeriya baki daya. Ameen

~ Comr Abba Sani Pantami

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button