BATUN SHUGABA MUHAMMADU BUHARI KAN ZABEN 2023.

Jam’iyar APC Ne Zata Sake Yin Nasara Ne A 2023, Saboda Irin Namijin Kokari Danayi Abaya, Cewar-Shugaba Buhari

Shugaban kasa Buhari ya bayyana cewa yana da tabbacin yan Najeriya zasu cigaba da zaben jam’iyyar APC, ya kara da cewa yana da wannan tabbaci ne saboda irin namijin kokarin da gwamnatin APC ta yiwa yan Najeriya.

Idan ba’a manata ba Shugaba Buhari ya hau mulki ne ranar 29 ga Mayu 2019 kuma zai sauka ranar 29 ga Mayu, 2023

Shugaba Muhammadu Buhari, a ranar Alhamis ya bayyana cewa gwamnatin All Progressives Congress (APC) ta yiwa yan Najeriya namijin kokarin da ya cancanci su sake zabenta.

Buhari ya ce gwamnatinsa ta yi aiki mai kyau musamman a bangaren aikin noma, gina tituna, ilmin ICT, da jin dadin yan Najeriya.

Ya baiwa yan Najeriya tabbacin cewa zai cigaba da karfafa demokradiyya a siyasa da jagoranci.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button