Labarai

RUNDUNAR YAN SANDAN JAHAR KANO TAYI NASARAR KAMO WANI MATASHI DAN DAM FARA.

Rundunar yan sanda ta jihar kano ta samu nasarar Kama wani matashi mai suna Gaddafi jibrin mai kimanin shekaru 33 dake unguwar tudun murtala a kano.

An samu nasarar kama Gaddafi ne Bayan Da Rundunar yan sandan Ta samu Korafi akansa cewa Ya canjawa wani mutum ATM yayinda ya Bashi na Bogi lokacin da ya nemi ataimaka masa wajen cire kudi.

Haka kuma an kama Gaddafi da ATM 22 da kuma mota kirar peaugeut wadda sukeyin amfani da ita wajen zagayawa wuraren da ake hada hadar kudi domin cutar al’umma.

Tuni dai Gaddafi ya amsa laifinsa kuma ana Neman sauran abokansa Ruwa ajallo kamar yadda kakakin Rundunar sp abdullahi Haruna Kiyawa Ya Sanarwa manema Labarai.

Kiyawa ya shawarci mutane da su daina Neman taimakon cire kudi ga Wanda Basu sani ba yana mai cewa su Rika zuwa da yan uwansu ko kuma su nemi ma’aikatan bankin domin taimaka musu.

Ana samun Nasarar kama irin wadannan Mutane Dake cutar mutane a Banki wajen sauya musu ATM da jabu wato marakyau.

arewanahiya

Farin cikinmu shine ganin farin ciki saman fuskarku muna alfahari duku masoya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button