WANI BANGARE A JAHAR NAIJA NA MURNAR GWANGWAJE SU DA SENATAN SU YAYI.

Yana da wahala a wayi gari ba tare da sanata Bima ya tallafa wa wasu daga cikin al’ummar sa ba.

A yau, ba zato babu tsammani ya zabo wasu matasa daga cikin al’ummarsa ya gwangwaje su da sabbin babura (machine) na hawa.

Wannan kyauta zai taimaka wa matasan wajan rage wahalhalun zirga-zirga nayau da kullum, sannan wasu lokuta zasu iya amfani dashi wajan neman abincinsu..

Wadannan suna daga cikin dalilai da yasa nake ganin ya kamata sanata Muhammad Bima Enagi ya jagoranci jahar naija baki daya a zabe mai zuwa na 2023.

Tsarinsa yana tattare da nuna kulawa da talakawansa. Kuma shi mutum ne mai qoqarin farantawa jama’ar da yake wakilta. Tabbas idan aka zabe shi a matsayin gwamnar jihar Naija muna da yaqinin zai kawo canji a wannan jahar tamu data jima tana fuskantar qalubale iri daban daban.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button