Labarai

RAYUWA KENAN ALLAH UBANGIJI YA JIKAN MAZA.

Allah ya jikan dattijan arziki rayuwa ke nan watarana sai labari yan maza ankwanta dama.

Yau shekaru 20 (4/4/2002-4/4/2022) da rasuwar Alhaji Muhammadu Adamu Ɗan Kabo, Jarman Kano, Hakimin Kabo, Turakin Pankshin, Sardaunan Kagoro, Oruwase of Urhobo land, kuma Adah Idah-ke Eburutu of Calabar.


Ya bada gudummawa wajen ci gaban arewa ƙwarai, harkar jirage, banki, tallafawa mabuƙata da raunana, da sauran su.
Allah ya jiƙan sa, ya ƙara masa rahama, amin.
Haka shima tsohon Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Muhammadu Abubakar Rimi, yau ya shekara 12 (4/4/2010-4/4/2022) da rasuwa.

Ya bada gudummawa ƙwarai wajen gina tsohuwar jihar Kano, kuma ɗan gwagwarmayar neman ƴanci ne wanda ba zamu manta dashi ba. Shima, Allah ya jiƙan sa da rahamar sa, amin.
Ya Allah, don albarkar wannan wata mai falala, ka jiƙan su, da duk waɗanda suka riga ƙu gidan gaskiya, amin.

arewanahiya

Farin cikinmu shine ganin farin ciki saman fuskarku muna alfahari duku masoya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button